FreeArewaPen original
ME 'DEBE KEWA
- 1views
- 29chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
💝 ME 'DEBE KEWA💝Writing By Amnah El Yaqoub1&2Garin Malam...Hadejia Area Jigawa State1986.Gidane d'an qarami wanda yake d'aukeda d'aki qwaya d'aya jal ginin qasa,be samu arziqin samun Katanga irinta d'akin ba,wato katangar qasa,saide yasamu arziqin samun katangar zana,ita kanta zanar da'akai katangar da'ita batakai har qarshe ba saida kara aka qarasa ta.Gidan abushe yake qaraf bashida komai face wata madedeciyar bishiyar maina me mutuqar sanyi,kana ganin gidan kasan gidan wani mashahurin talaka ne futuk wanda bashida cin yau bare na gobe.Kyakykywar mace me shekaru aqalla talatin da d'aya tagama share gidan daqyar saboda tsohon cikin datake dauke dashi me mutuqar girma haihuwa yau ko gobe,gumin fuskarta ta share,ta nufi qasan bishiyar gidan ta zauna tana maida numfashi tareda lumshe idonta tanajin dad'in is'kar datake kad'awa,jingina tayi da jikin bishiyar hakan yasa d'an kwalin dake daure akanta yazame yafad'i,wani uban gashi me sheqe da bala'in tsawo ya bayyana,gashin nata baqi ne sid'ik,ita kanta idan ka kalleta karon farko zaka tabbatar matar manya ce,asalin kalar farar fatarta zaisa kagane cewa ba 'yar Nigeria bace.Ahankali tajuya ta kalli d'akinsu da tsakar gidan wanda babu komai yaqare, babu abinda zata samu tasa acikinta,amma duk da haka cikin dauriya ta shafa qaton cikinta tace"kayi haquri kaji,Babanka zaizo yakawo mana abinci"Kafin ta dauke hannunta daga kan cikin,mijinta yashigo gidan bakinsa dauke da sallama,tun kafin ya qaraso inda take yagama qare mata kallo yana sake yiwa Allah godia daya azurtashi da Samun mace kamarta, yasan cewa banda qaddara da qudurar ubangiji itadin ba sa'ar aurensa bace,amma sai gashi ubangiji bai dubi hakanba, ya mallaka masa ita amatsayin mata d'aya tilo. Zama yayi kusa da'ita har jikinsa yana gogar nata,ya kalleta cikeda kulawa da tsantsar so sannan yace"Mai Gadon zinare yakike zaune kai babu dankwali?"Murmushi tayi dimples dinta suka bayyana,wanda suka sake qawata kyawun fuskarsa na asalin buzuwar qasar Nijar,cikin shauqin qauna tasaka hannunta tafara tattare dogon gashinta,cikin sauri yasaka hannunsa yana tayata tattare gashin,cikin jin dadi tace" Malam zafi naji,bansan lokacin da dankwalin yafadi ba,da alama de yau kasamo mana abinci,na ganka da farinciki"Murmushi yayi,sannan yasake gyara zamansa yana fuskantarta "wato Bilkisu duk lokacin dana tuna inada mace kamar ke acikin gidana,hankali na yana kwanciya,duk rashin kudi na da talaucina,inde na kasance tare dake kina 'DEBE MIN KEWA,kudi nasamo masu yawa har kimanin dubu biyu" ya qarasa maganar yana futo da kudin daga aljihunsa,ya ajiyesu agabanta.Kyawawan fararen idonta ta zaro,cikin tsananin mamaki dakuma ganin yawan kudin yasa ta kalli mijin nata tace"Malam Ina kasamo wannan kudaden masu yawa haka?""kekena nasiyar Bilkisu,lissafa kigani cefanan kwan...
App exclusive
Continue “ME 'DEBE KEWA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.