FreeArewaPen original
Matar shige
- 1views
- 63chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
MATAR SHIGE...!* _(Ba ta daraja)_BY *SADIYA ABDUL* _(Maizafafa)_*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️* Page 1 Ranar bakwai,ga watan d'aya,shekara ta dubu biyu da goma sha shida,ita ce ranar da littafin k'addarata ya fara bud'ewa,ranar da na shiga cikin damuwar da ba na tunanin zan fita har abada! Zaune na ke a cikin adaidaita sahu,kan hanyata ta komawa briged daga gidan yayata da ke unguwar hotoro,kaf hankali na ya na kan wayar da na ke amsawa ta masoyina,wanda yau watanni biyu ya rage auren mu."Y'an mata don Allah zan shiga nan,na kar'bawa maigidana sak'o"Na ji muryar mai adaidata sahunaSai na kai duba na ga laundry (wurin wanki)d'in da ya ke nuna min,na ce"ok" Tsautsayi ba ya wuce ranar sa,da na san zan ga abin da na gani yanzu me zai fito da ni yau? Wata bak'ar mota ce ta ke k'ok'arin fakin a wurin,duk da ban san tsadar motoci ba na san wannan dai ba k'arama bace,ya yi minti uku da fakin ga shi dai ya bud'e murfin motar amma bai fito ba,haka ne ya sa ni sake tattara duk hankali na wurin ganin wannan mashahurin. A kan idona ya fito daga cikin motar,gabana ya fad'i daga yi masa kallo d'aya tak!Fari ne tass,mai manyan idanuwa ,farare tas kamar bai ta'ba yin kuka ba,ba wani dogon hanci ne da shi ba,madaidaicin bakinsa ya hau sosai da zagayayyiyar fuskarsa,Bak'ar riga ce a jikinsa da bak'in wando iya k'wauri,ga wani bak'in agogo da ya yi wa farin hannunsa kyau sosaiBa k'aramin tafiya da imanina ya yi ba,nan take na ji wani irin yanayi a zuciya da gangar jikina,na yi wata kasalalliyar ajiyar zuciya,ina kuma k'are masa kalllo Yamutse fuska na ga ya yi,tare da kai hannunsa kan gashin kansa da ke ta shek'i da alama ya sha gyara har ya gaji,ya wani hautsina sumar wanda na ji kamar da gayya ya yi,don kuwa wani irin kyau na ga ya k'ara,kai ka ce ba d'an Nijeria ba ne,wallahi ban ta'ba zaton a kwai irin kyawawan nan a garin Kano baMota ya koma,ko shiga ciki bai yi ba hannu kawai na ga ya mik'a ya ciro wata jar facing cap ya saka. Wanda ya yi daidai da dawowar mai adaidata sahu na,hannunsa d'auke da wata jaka Ina kallo matashin ya shiga wurin,ya na ta b'ata rai. "Yi hak'uri hajiya,na 'bata miki lokaci" Mai adaidaitar ya fad'aNa yi guntun murmushi lokacin da mu ke wuce wurin na ce"babu komai" Sai da mu ka d'an yi tafiya,na ji muryarsa"sunan shi Salim,shi ne mai wurin wankin nan,kuma shi ne me wurin cin abincin nan na sabin sati(seven thirty) ba shi da kirki,kuma ya na shan sigari,an ce ya na da kamfani a sharad'a,wanda da kan shi ya ke kula da shi,kuma gidan su ma a can ya ke" Ban yi mamakin maganganun sa ba,don na san ba ya rasa nasaba da irin kallon da ya ga ina yi wa wanda ya kira da Salim d'in "Hmm!" Na sauke a...
App exclusive
Continue “Matar shige” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.