FreeArewaPen original
SHAAMEEƘH na Uwar Batoorl
- 1views
- 57chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwar batoorl ✍️ writer Follow me on Whattpad - @Uwar batoorl *** *** *** Gmail - ***
Sample · Shafi na ɗaya
🕊️ SHAAMEEKH 🕊️ B̶̶O̶O̶K1 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) 𝘔𝘈𝘙𝘜𝘉𝘜𝘊𝘐𝘠𝘈𝘙 '𝚈𝙰𝚁 𝚂𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙲𝙴𝙴! Paid #300 '𝚈𝙰𝚁 𝙺𝙰𝚁𝚄𝚆𝙰! Free 𝙹𝙰𝙷𝙸𝙻𝙲𝙸 𝙺𝙾 𝙰𝙻'𝙰𝙳𝙰! Paid #500 𝙼𝙰𝙵𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙽𝙰𝙷! Free ᴀɴᴅ ɴᴏᴡ𝘚𝘏𝘈A𝘔𝘌𝘌𝘒𝘏 🕊️ PAID #500𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍Ina mai godiya ga Allah da ya bani iko da daman fara wannan sabon littafin nawa mai suna SHAMEEKH, Allah sa mu kammala lafiya, duk abinda ya ke ba dai-dai ba a ciki Allah ya yafemu duka, ni mai rubutawa da ku masu karatu, FAN'S ina matuƙar ƙamnarku, Uwar batoorl na mugun yinku irin sosai ɗin nan, masu daraja habibties.SADAUKARWA NE GARE KU Masoya alƙalamin Uwar batoorl.TUKUICI NE GARE KASIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci) Da kuma ɗaukacin member's namu.GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE!.̶ ̶F̶r̶e̶e page Mareeyata wannan page naki ne kiyi yacce kike so da shi, Uwar batoorl na jinjina miki da sharhinki.Shafi Na Ɗaya. ⭐ DUBAIkwance yake a makeken haɗaɗɗen gadonsa wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, lulluɓe yake da blanket mai shegen laushi ya rufe dukkan ilahirin jikinsa ko ɗan yastansa ba ka hangowa, ba abinda ke tashi a hamshaƙin haɗaɗɗen daƙin nasa sai wani arnen ƙamshi mai sanya nistuwa, da kuma sautin ac wanda ya taimaka wa ƙamshin wajan jefa duk wani halitta da ke cikin ɗakin a yanayi mai daɗin gaske. Wayansa dake saman bedside drawer ne ya fara ringing, waƙan jimmy na Colorado ne ke tashi yayinda wayan ke kan kukan neman agaji! 𝙈𝙮 𝘾𝙤𝙡𝙤𝙧𝙖𝙙o! 𝙮𝙤𝙪'𝙧𝙚 𝙢𝙮 𝙩𝙤𝙣𝙮𝙞 𝙢𝙮 𝙩𝙤𝙢𝙖𝙩𝙤! 𝙢𝙚 𝙞 𝙜𝙤 𝙩𝙖𝙠𝙚 𝙮𝙤𝙪 𝙩𝙤 𝙨𝙬𝙚𝙚𝙩𝙤!𝙮𝙤𝙪'𝙧𝙚 𝙢𝙮 𝙨𝙚𝙫𝙚𝙣 𝙢𝙮 𝙧𝙤𝙣𝙖𝙡𝙙𝙤! 𝙚𝙝𝙝! 𝙚𝙝𝙝! 𝙢𝙮 𝙜𝙚𝙡𝙖𝙩𝙤𝙤!!! Ƙiran ne ya tsinke, ba jimawa wani ƙiran ya kuma shigowa, sai lokacin wanda ke cikin blanket ɗin ya ja siririn tsaki tare da mirginawa ya gyara kwanciyan sa hankali kwance ba ko alamun zai bi ta kan wayan balle mai ƙiran ya samu arziƙin a amsa masa. Bayan second's sai wayan ta kuma sanya kukan neman agaji, wannan karon wanda ke cikin blanket ɗin a yangance kaman ba ya so ya miƙo haɗaɗɗiyar hanunsa ya sanya wayan a silent, hannunsa ya maida cikin blanket nasa dan yasan yanzu kam zai yi bacci hankali kwance. Bayan kaman mintuna talatin har bacci ya fara awun gaba da shi, kaman a mafarki ya kuma jiyo kukan ɗayan wayansa dake kan gadon a kusa da shi, ringing tone ɗin kawai ya isa ya sanar da kai wanda ke ƙiransa, domin waƙan Sim...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.