FreeArewaPen original
'YAR KARUWA na Uwar Batoorl
- 1views
- 7chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwar batoorl ✍️ writer Follow me on Whattpad - @Uwar batoorl *** *** *** Gmail - ***
Sample · 1-5
👄'YAR KARUWA👄💅 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍Ina mai godiya ga Allah da ya bani iko da daman fara wannan sabon littafin nawa mai suna 'YAR KARUWA, Allah sa mu kammala lafiya, duk abinda ya ke ba dai-dai ba a ciki Allah ya yafemu duka, ni mai rubutawa da ku masu karatu, FAN'S ina matuƙar ƙamnarku, Uwar batoorl na mugun yinku irin sosai ɗin nan, masu daraja habibties.🥰SADAUKARWA NE GARE KI Baby batoorl (my unborn favorite soul)TUKUICI NE GARE KASIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci) Da kuma ɗaukacin member's namu.PAGE NA FARKO DA KU ZAN FARA KAMAN YANDA NA YI ALƘAWARI. Masoyiya Bealkysou Ummu Adeel tawan 🅿️ 1 _ 5Matashiyar yarinya ce zuƙeƙiya fara, farinta dai-dai, 'yar kimanin shekaru 20 da haihuwa, durƙushe take akan guiwowinta ta yi kneel-down a gaban wata mata wacce ko ba'a faɗa ba kasan mahaifiyarta ce duba da kaman da suke yi da kuma maganganun da matashiyar budurwan ke yi. Cikin tsananin kuka mai nuni da stagwaran taƙaici da kuma tsaban damuwan da take ke ciki ta ce, "Haba Mami na, Mami dan Allah dan Annabi ba dan ni ba, kuma ba dan halina ba ki bar wannan rayuwa, Mami kina zubar da mutuncin kanki kina zubar da na 'yar ki, Mami da girmanki kina rayuwa irin ta yara ƙanana marassa tunani ko mafaɗi, Mami ke fa ya kamata ki stawatar mini idan kinga ina ƙoƙarin sanya kai na a irin wannan lalatacciyar rayuwan, amma fa Mami ke da kanki kike yi ba ma ni ɗin ba, haba Mami na ina iliminki da tunaninki kika zaɓa mana wannan rayuwa irin ta jahilai...." Maganan dake baki na ne ya maƙale a maƙoshi na, sakamakon wani azababben marin da Mami na ta kifa mini, miƙewa tayi tsaye tana huci ranta a ɓace kaman ko da yaushe idan hakan ya faru tsakaninmu, idanuwanta ta zuba mini tare da cewa, "BANAFSHA har rashin kunyar ki da fistaranki sun kai haka? Ina mahaifiyarki kina sokamun baƙaƙen magana, ni kike faɗawa ina rayuwa irin ta jahilai? Ni kike ƙira jahila Banafsha? Irin tarbiyyan da na miki kenan ki nunawa duniya ni ma kin renani balle wasu? Banafsha ni kike faɗa wa haka?" Mami ta ƙarishe maganan cikin stananin ɓacin ran da har idonta na ƙoƙarin sauya kala. Cikin kukan da ya zamo mini jiki dan in da sabo na saba, sai na ce, "Allah ya huci zuciyanki Mami na, amma wuyana bai yi ƙwarin da zai sa nayi suɓutan harshe a kan mahaifiya ta ba, koma menene ke ɗin uwa ce a gare ni kuma ko ya kike ke mahaifiyata ce, amma ina mai haɗa ki da Allah da Manzon sa Mami kiji tausayin rayuwata kibar wannan lalatacciyar rayuwan, munanan maganganun da mutane ke jifa na da shi tun baya damuna har ya fara mini ciwo, Mamina dan Allah kiji tausayin maraici na ki daina wannan ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.