ITA CE ƘADDARA TAFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

ITA CE ƘADDARA TA

  • 1views
  • 42chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1

Aje ayi following din mu yan amana. Tiktok Account *** 𝑪𝑬 𝑲𝑨𝑫𝑫𝑨𝑹𝑨 𝑻𝑨* ByHusaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah)Paid book Free page #Romance#Ban dariya#Tausayi 1 *SHINFIDA*Rayuwa tamkar tafiya ce ta kaddara. Kowane ɗan Adam yana da nasa littafin da aka rubuta masa tun kafin a haife shi. Akwai waɗanda kaddarar ta zamo musu alheri, akwai kuma waɗanda rayuwarsu ta cika da ƙalubale da jarabawa. Wannan labari ya ta’allaka ne a kan yarinya ƙarama wadda ta taso a gidan kakarta bayan ta rasa Mahaifiya.A hannun kakar ta ne ,ta tashi ba tare da kulawa da tarbiyya ba, hakan ya jefa ta cikin rayuwar da ba ta da tsari. Babu kamu, babu ladabi, babu nutsuwa,ta shahara wajen rashin kunya da wulakanta kowa, ko babba ko ƙanƙani. Kazanta ta zame mata ado, rashin hankali ya zame mata kwalliya.Sai dai duk da haka, rayuwarta ta kasance wata ƙaddara da za ta zama darasi ga mai karantawa: shin za ta ci gaba da tafiya a kan wannan tafarkin da zai hallaka ta, ko kuwa za ta fuskanci canji wanda zai ɗora ta kan hanyar da ta dace?.“Ita Ce Ƙaddara Ta” labari ne da ke bayyana irin tasirin da rashin tarbiyya da kulawa ke da shi ga rayuwar yara, da kuma irin jarrabawar da kaddara ke jefa ɗan Adam ciki. 001Abeji wani ƙauye ne da yake cikin ƙaramar hukumar Kuje a Abuja. Yana daga cikin ƙauyukan da har yanzu jama’arsu suna rayuwa da harkar noma da kiwo, musamman shanu, tumaki, kaji da kuma amfanin gona irin su masara, dawa, gero da wake.kauye ne da ya tara dadtawa da yara matasa, lokaci kaka ne yasa duk wata hanya da zaka bi in dai ta raɓi gona zaka ci karo da Shuka wace shafi yanayi kaka ga iska ta fara busawa. Abeji kukan tsuntsaye shine zai sa ko baka so ba,za kaji Abeji ta burge ka.Karfe Shaɗa agogo Nigeria yake bugawa wanda yasa babu kowa duk wani matashi da maza sun tafi gona dan gyara anfani gona hakan ya dada samar da shuru cikin gari. Gidan Kakar Lana shine me babbar ƙofa kato ƙyaure ne ma ƙale jikin kofar duk da an buɗe kofar han hakai, tsohuwa me kima Ni shekara 70 fara duk da tsufa ya cin mata take kwashe sabon wake da ta shanya shi a rana. Cikin faɗa da babu kowa afili tsakar gidan wanda ya ci malale suminti take faɗa“Sai da nace da Lana kar ta je gona ama ta kafe sai taje yanzu ko yaushe zata dawo ta karbo mana Niƙan dan wake?Gashi har rana ta garje.”ta faɗa tana shigar da Waken wani ɗaki da yasha tayis, wanda duk kusan kayan an fani gona ne na wacan damuna.daki ta koma da rediyo ta ahannu.gona ce banda ihu da waƙar masu tsinkar gyaɗa babu abin da kakeji.Muryar da ta zarce ta kowa kauɗi kake ji cikin salon na waƙe.*“𝑴𝒂𝒌𝒐𝒓𝒊-𝒎𝒂𝒌𝒐𝒓𝒐𝒓𝒐”*Sukuma sauran yaran yan tsikar gyaɗa suna mata amshi da cewa“𝑨 𝒘𝒖𝒚𝒂𝒏𝒂!”𝑩𝒂 𝒂𝒘𝒖𝒚𝒂�...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “ITA CE ƘADDARA TA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play