MURADIN RAI!Free

ArewaPen original

FantasyFreeOngoing

MURADIN RAI!

  • 1views
  • 17chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · The Weight of Destiny

💫MURADIN RAI!💫بسم الله الرحمن الرحيم Page: 2Ya na faɗuwa Ƙarar ihunsa ya sauka a kunnuwan wani dattijo wanda ya fito ran gadi tareda masu yi masa hidima. da ga kallon farko idan kai ma sa zaka fahimci ya fara manyanta,  a ƙalla  shekarunsa za su haura hamsin da biyar geting to 60.Amma ya nayin jikinsa bai nuna hakan ba, saboda wada da jin daɗin dukiyar da ya ke da ita. dattijon bai kasance  cikin jerin masu duhun fata da ƙiba ba, mutum ne mai cikar zati da haiba, fuskarsa a zagaye ta ke da farin gemu wanda ya yima bakinsa ado.Wannan ya sa launin gashin ya ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini.  a hankali ya ke takawa guards ɗinsa suna take masa baya, sanye ya ke cikin wata kakkaurar sweater mai launin makuba. Sosai rigar ta bi lafiyayyen jikinsa ta kwanta tamkar don shi aka samar da ita.Su na ƙarasawa inda yaron ke kwance dattijon ya sunkuya ya na mai ƙarewa yaron kallo. da hanzari ya maida kallonsa ga matasan da ke take ma sa baya ya ce "Take him to the hospital, he doesn’t seem to have much strength left." ya faɗi hakan ya na kai hannunsa fuskar yaron.Da sauri ɗa ya da ga cikin guards ɗin ya kinkimi Hateym dake kwance babu numfashi, ya nufi ɗaya da ga cikin manyan motocin da su kai perking a jejin. Ya na shirin buɗe motar  ya tsinkayi muryar Mr. Uty Dodo ya na tambaya "da ga nan zuwa Asbiti ze ɗaukeka minti nawa ne?"Cikin girmamawa matashin ya ce "kimanin awa guda Ranka ya daɗe." Uty ya ja numfashi sannan ya kalli tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce " idan Headquarter ɗin mu zaku kaishi zai ɗaukeka minti nawa ne?"A hanzarce matashin ya ce "It’s thirty minutes, Your Highness."Murmushi ya yi sannan ya ce,"Take him to the headquarters since it’s closer, and make sure he receives all the necessary assistance until he regains consciousness." Cikin girmamawa ya amsa da"Your command is my duty to fulfill, Your Highness." sannan ya buɗe bayan motar ya kwantar da Hateym, shi kuma ya shiga mazaunin driver ya tashi motar da gudu ya bar gurin don cika umarni.Tun kafin su isa headquarter ɗin Hateym ya farka kansa na juyawa, still hannunsa riƙe da ƙaramar jakar da mahaifinsa ya ɗaura masa tamkar rai da Ajali.A hankali ya yi yunƙurin tashi, amma ƙafarsa ta yi masa nauyi saboda cizon kunama ta yi masa bayan fitowarsa da ga cikin kogon dutse. Sai da ya ja numfashi sau uku kafin ya yunƙura ya miƙewa ya zauna, yana kallon mutumin da ke tuƙa motar.Mutumin ya na juyawa su kai ido huɗu da Hateym, sai ya ɓare baki ya na kiran, "Daddy… Daddy where are you?" kuka sosai ya ke yi ya na kiran babansa.Gefan titi matashin ya gangara ya parker motar, sannan ya buɗe motar ya fita ya zagaya bayan motar yana kallon yanda ya ke kuka bakinsa duk ya bushe. Hannu ya miƙa masa amma Hateym ya maƙe kafada tareda ƙanƙame jakarsa.Mama...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “MURADIN RAI!” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play