FreeArewaPen original
KU YI MANA ADALCI
- 1views
- 52chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
*KU YI MANA ADALCI* NA Sadiya Abdulrazak Page 1Marubuciyar Aure A Yau Sandar dukan uwargida Ranar KukaMiji gomaZuciyar maceIya ruwaWani aurenDa Walakin Wutar Ƙaiƙayi Matar shige. Dss Duniya juyi-juyi, kawaɗo ya faɗa a ruwan zafi, ina yawan tunawa da wannan karin maganar cikin zuciyata, saboda a yanzu dai yana taka ta shi rawar a cikin rayuwar aurena. A baya idan wani ya ce mini zan iya yin bacci ba a kwance a ƙirjin mijina ba alhalin muna kwance a gado ɗaya, zan shiga shakkun tabbatuwar hakan, inda a ce wani ya taɓa faɗa mini akwai ranar da za ta zo muna gida ɗaya da mijina mu raba ɗaki kowa ya kwana shi kaɗai a na shi ɗakin wallahi nan take zan daka tsalle na musa cikin isa, amma sai ga shi zamani ya jujjuya da rayuwar aurenmu ya watso mu ƙadamin da muke ciki a yau, wanda ya fi kama da rayuwar maƙiya ba masoya ba. Juyi na yi a makeken gadon nawa, na lalubo filo na rungume, ina sane da hasken wayata da yake ta kawowa a karo na babu adadi, alamun mai kiran wayar har yanzu bai gajiya ba, na mirgina na kalli wayar, ba don neman sanin mai kiran ba, don na san wannan, agogon wayar na duba wanda ya nuna ƙarfe sha biyu na dare da minti goma, idan na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, sai yanzu Sadam ya gama waya da chatting ɗinsa da matan da yake ganin sun fi ni daraja a halin yanzu, wanda nake ƙarfafa zargin sun kunna shi ne, yake neman yadda zai kashe wannan wutar ta wajena, don haka na ƙudure ba zan iya amsa kiransa ba, duk da ban manta da hukuncin matar da mijinta ya kira ta shimfiɗarsa ta ƙi amsa kira ba. Ina sane ƙofar ɗakina a buɗe take, don haka shigowarsa ba ta ba ni tsoro ba, amma ta ba ni mamaki, nan take na tuna da rantsuwar da ya taɓa yi mini a ranar da nake kuka ina tabbatar masa ba zan sake kwana a ɗakinsa ba, ya ce"Na rantse da Allah Sayyada babu macen da ta isa na bi ta ɗakinta na kwana da ita, kuma tun da ni mijinki dole ki amsa kirana a duk lokacin da na buƙaci hakan".Shin na karya masa rantsuwarsa ne tun ba a je ko'ina ba? Lumshe ido na yi kamar mai bacci, daidai lokacin da ya kai hannu ya kunna globe ɗin ɗakin, ya taka a hankali ya ƙaraso ya zauna a gefen gadon "Sayyada, Sayyada".Ya shiga kirana da taushin murya kamar munafiki, ban ko motsa ba, don haka ya kai hannu ya fara taɓa fuskanta, na janye hannun na shi da sauri tamkar wanda ya taɓa ni da bakin wuta, ya riƙe hannun nawa ƙam ya jijjiga shi sannan ya ce"Tashi mana, ina ta kiran wayarki ashe kin yi bacci".Na fizge hannun na ce"Ban yi bacci ba, zuwa ne ba zan yi ba! Kenan ba ka yarda ba da na ce maka ba zan sake kwana a ɗakinka ba ko?"Ya sauke numfashi, har yanzu da wannan sanyin muryar wanda yake yaudarata da shi a da, ya ce"Haba Sayya...
App exclusive
Continue “KU YI MANA ADALCI” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.