FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
TAZARAR SO ByNafisa S Adam(Nafsal KZ)KARAMCI WRITERS ASSOCIATION(Karamci Tushen mu'amula ta gari) Page 1"Atika Atika Atika" malam Tasi'u ya shigo gidan yana faman kira ba tare da ya yi sallama ba. "Na'am Malam, wannan kiran ai yayi yawa sai ka bani tsoro, kamar wani zararre". Atika da ta fito daga ɗakinta ta faɗa tana gyara ɗaurin zanenta."Wato Atika ni kike kira da zararre ko, to wallahi sai dai ki nemo mai hankali ya je ya nemo muku abinda zaku ci a gidan nan" Malam Tasi'u yayi maganar cike da ɓacin rai"Wayyo Malam kayi haƙuri, suɓutar baki ne, ai bamu da wanda ya fika".Malam Tasi'u na harhaɗe rai ya miƙawa Atika ledar dake hannunsa yace "Ga shinkafa nan rabin kwano ce da Ƙyar ma na samota dan haka kowa yaci ya batse da ruwa".Ledar Atika ta kalla tace "To wannan ai ko ni da yarana ba zai ishe mu ba balle na...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.