FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Muslimah.
Sample · 1
ShimfiɗaFitowa ɗaya motar tayi daga inda ba a zata ba. Babu wani ƙarar birki da ke jan hankali, kawai ƙarar bugun haɗuwar ƙarfe da ƙarfe kake ji da sauri-sauri sai wata kiɗa ta masifa. Illar ƙarfin bugun yasa gilashin motar tarwatsewa nan take, ya bazu cikin wani hazo mai kaifi da fushi. Jikin motar duk ya dushe yayin da motar ta tashi sama a iska ta faɗa da ƙarfi cikin wani rami dake gefen hanyar.Daga nan wani shiru mai firgitarwa ya ziyarci wurin. Tuni rediyon motar dake kwararo surutu ya daina aiki. Babu cigaban hirar dake gudana a gidan rediyon. A cikin 'yan daƙiƙu kaɗan, komai ya sauya.Ɗaya motar, wata babbar mota mai nau'in canter har yanzu tana kan hanya, gaban ta ya lanƙwafe kamar hancin alade. Abin mamaki engine ɗin motar har yanzu yana aiki duk da cewa ƙarar engine ɗin ya raunana kamar tarin tsohon da ya gaji, amma dai yana aiki. Na ɗan wani lokaci, fiye da lokacin da aka ɗauka wajen halaka rayuwar da ke cikin ɗaya motar, Direban motar na zaune yana rawar jiki yana riƙe da steering wheel na motar. Rana na daɗa haskakawa ta cikin rassan itatuwa. Har yanzu safiya ce mai cike da kyau da ƙayatarwa, kuma har yanzu hanyar shiru babu kowa babu alamar gifatawar wani bil-adama.Har a lokacin hanyar babu kowa. Babu shedun gani da ido. Shiru babu komai.Kusan mil ɗaya daga gida kenan. Direban ya fawwala komai ga ƙaddara. Idan har motar zata iya cigaba da tafiya, to Direban ya tabbatar zai tafi ya bar wurin ba tare da ya waiwaya ba. Idan kuma ba zata tafi ba, zai tsaya ya fuskanci sakamakon. Hannun sa mai tsananin rawa saboda firgici yasa ya danna gear sannan ya sa duka hannayen sa ya dafe steering wheel da ƙarfi, sai yanzu yake jin ciwo da raɗaɗin buguwar da ya samu a sassan jikin sa.Motar mai ƙirar canter tuni ta fara mirginawa ta fara tafiya da ƙyar tana karkatuwa zuwa komawa ga titi.Direban ya kalli bayan sa izuwa ga ɗaya motar. Hannu ya hango an ɗan ɗago da ƙyar daga cikin motar a kujerar fasinja mai zaman banza. Sai wani sautin kuka na neman taimako da yake jiyowa.Kasa jurewa Direban yayi ya fidda wani sautin gurnani. Zai nemo taimako. A duk inda Allah Ya haɗa sa da mutane zai nemo taimakon gaggawa a bawan Allahn dake ɗago masa hannu daga cikin ɗaya motar. idan kuma har haka bata samu ba, ya tabbatar wani zai zo nan ba da daɗewa ba.Wannan hanyar tana cika da mutane kafin tara na safe. Wani zai taimaka. Yana da tabbaci da hakan.
App exclusive
Continue “NA'EEMA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.