FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
'Yan uwa Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar suSandal flakesHaweeGabgabHalutDorot Coconut chipsDufr(farce)Black khumraBrown khumraWhite khumra Oil perfumes da Body spraysDan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar hakaCall/*** ***Location:Gonan Ganye,zariaKaduna state Nationwide Delivery1SHIMFI'DA.Sunana Amina Malam Salisu wanda ake kira da (Mai wankin hula) Ni tela ce k'wararriya sannan kuma malamar makarantar boko ce ta gomnati. Ina koyar da yara harshen hausa a firamare ta gwale local goment. Bazawara ce ni a yanzu mai yara biyu dukaninsu maza. Babban sunansa Kamalu sai d'an'uwansa Yusuf wanda muke kiransa da Yusi. Mahaifinsu ya rasu shekaru hud'u da suka gabata tun lokacin Yusi din yana da shekaru bakwai a duniya. Tazarar da take tsakaninsa da d'an'uwansa Kamalu ta shekara daya ce. Ni da Babansu Allah ya jikansa da rahama muna hasashen daga yin arb'anin din haihuwar Kamalun ne na yi katari da cikin Yusuf din. Tsiran da yake tsakaninsu dai bashi da wani yawa. Yanzu Kamalu yana da shekara goma sha biyu, yayin da Yusi yake da goma sha d'aya.Tun bayan rasuwar Yaya Aminu mahaifin yarana na koma gidanmu da zama domin dama gidan da muke zaune dashi na haya ne kasancewar akwai rashin 'karfi da rashin 'kwa'kkwarar sana'a daga 'bangaransa. Cikin ikon Allah sai aka yi sa'a d'akin da muka yi 'yan matanci ni da 'yan'uwana yana nan sai dai shirgi da matan gidan suke ajiyewa. Anan na ra'kube da 'yan kayana na zauna nake gurgura rayuwar kafin mu ga hukuncin da Allah zai zartar. Zamantakewatar auran da muka yi ni da Yaya Aminu na tsayin shekara goma sha uku kusan ni ce 'karfin gidan saboda Allah ya ri'ka mini Ina aiki, sannan ina d'inkin mata da 'yan gyare-gyare, bayan haka kuma ana kawo mini aikatau na jaka 'yar pose da huluna irin na yadin hijabai. Sosai Allah ya huwace mini. Duk wata zan d'auki albashi sana'ar d'inkin da nake yi kuma tana taimaka mana sosai har mu iske sabon wata ba mu galabaita ba.Ban ta'ba yin nadama ko na ji wani abu na 'kyashi a raina ba a duk lokacin da Ya Aminu zai nemi wani abu a wurina muddin ina dashi babu jayayya ko gardama nake d'auka na bashi. Babban burina ace asirinmu ya rufu gabad'aya, kuma dama tun lokacin da muka yi aure na yi alkawari cewa 'In dai Allah ya ri'ka mini sai Ya Aminu ya fi karfin komai a wurina, sakamakon irin hallacin da ya yi mini a rayuwata. Duk da cewa albashina bashi da wani yawa kasancewar firamare nake koyarwa, amma ana yin salary nake ware masa kudin transport, tun bayan korarsa da aka yi a kamfanin da yake aiki sakamakon tashin ciwonsa, to sai ya koma kasuwa yake buge-buge. Dalil...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.