FreeArewaPen original
SADAUKARWAR SO.
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 01
SADAUKARWAR SO..!!(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)***:@Jamilaumar315Mallakar:Jamilaumar(Janafty)HAKKIN MALLAKA⚒️🚫Wannan Labarin Gabadayansa Mallakata ne juyasa ko Sarrafashi ta sigan maidashi Audio ko kuma Sakashi a Youtube Channels ko kuma Daukansa Zuwa wani kafar sada Zumunta batare da Izinina ko Sanina ba❌Littafin Da Duka Labarin mallaki na ne...!🙅Bismillahir Rahmanir Rahim in the name of Allah The most Beneficient the most Mercefull praise be to Allah load of The wordsPage1️⃣KANO STATE..*Doguwa Local goverment.*AREA:RiriwaiSHIMFIDA.."A karamar Hukumar Doguwa Dake Jahar Kanon Dabo a Wata anguwa mai Dauke da Gidaje masu karamin karfi na Hango Wani Karamin Gida na Ginin kasa da Misalin karfe 3:30pm na Talatainin Dare da Hasken Fitila Daga Tsakar Gidan da alamu wani Abu na Faruwa agidan Har takai masu Gidan basu saka Hakarkarinsu a kasa ba Domin kwanciya ba,kila saboda wani yanayi ko Rashin Sukunin Danayi Hashashen Mazauna Gidan mai Dauke da Shashe Guda Biyu Da ke matsaikacin Gidan.Wani Matashi ne Domin akallah zai kai Kimamin Shekara Talatin da Biyar a Duniya ayanayinsa Dogo ne Mai Cikar Ingarman Jiki Da kwanji Kallo Daya zakamai ka Fahimci ba Rago bane Domin akwai Tsantsan Jarumta irin ta Manoman kauye Tare Dashi Fari ne sai dai Wahala Irin ta Mazauna kauye yasa Kalarsa ta koma Duhuwa,wanda ya Sauya ya bada wani kala Dabam.Safa da Marwa yake yi Kofar wani Daki Wanda yaji Filista da Shafan Farin Fenti Hannayensa Suna Goye a bayansa ne yadda yake Safa da marwan bakinsa na Motsi Alamun baya Cikin Natsuwa akwai Tashin Hankali Karara a Fuskarsa Da Hasken Jan Lantarkin Dake Bakin Kofar Dakin ya gama Gauraye Karamin Tsakar Gidan ya haskashi gabadaya.Wata Yar Dattijuwa ce ta Yaye Labulen Dakin Ta Fito Lokaci Daya Tana gyara Haban Zaninta a kallah Ashekara bazata gaza 58 ba Sai dai kallo Daya zakayi mata kasan Tana da alaqan Jini mai karfin Tsakaninta da Matashin Dake Safa Da marwa abakin Kofar.Yana ganin ta Fito Da Hanzari ya Isa Gareta yana Fadin"Innanmu..Innanmu..Ya ake Ciki..?Ya Fada Cikin karaya da wani Fargaba wanda kallo Daya zakayi mai Kaga alamun Hakan ya Bayyana a saman Fuskarsa.Inna Hasiya ta Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana kallon Fuskar Dan"ta Habibu Daya Gauraye da Fargaba da Tsausayin Halin da mai Dakinsa Take Ciki Cikin son kwantar mai da Hankali Ta Rike Hannayensa Duka Biyu Tana Fadin"Har yanzu Bata Sauka ba Habibu..Ammh Tana kan gwiwa Insha Allahu yanzu Zata sauka Kadaina Damuwa Kaji ko..?Cikin Karaya ya Girgiza kai yana Fadin"Innanmu Ko Zan Fita na samo Mota ne mu kaita nan General Hospital mugani..? Kai ta Girgizamai kafin ta samu Zarafin Mgana sukaji Numfashi mai karfi da Salati lokaci Daya Muryan Hajara ya Gauraye Gidan Inna Hasiya ta Saki Hannu Habibu Ta Fada Dakin Shima kamar ya Bita Haka yaji ammh Ba Dama sa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.