FreeArewaPen original
TUN RAN GINI
- 1views
- 72chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci ba makaryaci ba ne
Sample · Chapter 1
DA SUNAN ALLAH MAI RAhMA MAI JIN ƘAI.SANIN GAIBUPAGE ONE*MARYAM LITEE"Ki bar ma Halima wanke-wanken ki tafi zuwa zancen ai ya fi muhimmanci."Kalaman da na tsinkaya kenan daga bakin mahaifiyata tana faɗa ma ƙanwata A'isha da aka aiko ana kira a waje.Na dubi tulin wanke-wanken na dubi igiyoyi biyu da na cika da shanya kayana da na mahaifiyar tawa da na ƙaramar ƙanwata Bilkisu, gabaɗaya na gaji so samu na samu wurin da zan yada haƙarƙarina na huce tarin gajiyar da ta yi wa ilahirin jikina ƙawanya tare da ciwon marar da ke murɗa mini akai-akai da nake tunanin na mene ne don baƙona lokacin dawowar shi da saura.A'isha ta yi fara'a jin an raba ta da wanke-wanken sai dai tana cira ƙafa na ce "Idan kin dawo kin yi abin ki a gajiye nake."Wani kallo Mamanmu ta feso mini kafin ta furzo mini maganar da ta haddasa ma ƙirjina riƙewa."Har wata gajiya gare ki Halima? Mu ba mu faɗi gajiya da ke ba muna za...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.