FreeArewaPen original
YAƊIN MAGE...
- 1views
- 40chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Shafi na ɗaya
U M M U A F F A N 2026YAƊIN MAGE...BOOK 1©FATIMA SUNUSI RABIU Ummu AffanHAƘƘIN MALLAKA: Ummu AffanGODIYA: Ta tabbata ga sarki Allah gagara misali, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S A W)JINJINA.Har kullum gare ku take iyayena, abin alfaharina Allah ya ƙara muku lafiya.SHAFI NA ƊAYAƊANDUME JIHAR KATSINA.Unguwa Gangare.Gidan Abulle.Ta muskuta daga zaunen da take, kana ta dube ta ba yabo babu fallasa ta ce."Hmmm! Wai Abulle me ki ke son ki ce ne? Nufinki ba ni da hankali ko ban san abin da nake ba?"Tana faɗa kuma ta miƙe tsaye, tare da gyara fallan zanin da ta ɗaura a kanta, wanda ake rufawa matsayin mayafi a shekarun baya. Abulle wacce take kallon Suwaiba baki buɗe ta ce,"Ba dai tafiya zaki yi ba?"Ba kuma ta jira amsarta ba ta ɗaura da cewa."Ban ga fa laifinki ba Suwaiba, kuma ba na jin har duniya ta naɗe zan iya ganin laifinki a wannan fagen, a...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.