FreeArewaPen original
Mijina Ne!
- 1views
- 54chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 01
Da hanzari ta tsallaka titin dake gabanta, gudu take kar ace ta makara, kar wani abu ya samu tilon y'arta. Yanzu idan wani abu ya faru da Hanan ina zata saka rayuwarta? Hawayen dake zubowa saman kuncinta tayi kokarin sharewa a hankali. Zata daure, Insha Allahu duk ynda zatayi dole ne ta sama ma kanta yanda zata sama ma Hanan lafiya. Tsayawa tayi bakin kofar asibitin tana kallon shige da fice na mutane. Wasu suna fita da ihu da kururuwa alamar wani nasu ya rasu, wasu kuma suna dariya alamar lafiya ta samu. Wasu kuma suna shiga cikin rudu, firgici da tunanin yananin da dan'uwa ko yar uwarsu take ciki. Duniya kenan, nan ita yanda take a hakan tana ji duniya ta mata kunci, wani nacan yau yake farin cikin da bai taba irinshi ba. Share hawayenta ta karayi tana mai kokarin fitar da murmushi saman kyakyawar fuskarta, wacce a yanzu idan ba mutum ya kura mata ido ba bazai taba cewa tana da kyau ba...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.