FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · RAI DA BURI 1
*RAI DA BURI*Episode 1By Maman shaheedPaid book ne,akan 700₦ mai son karantawa cikin Lumana Akwai a Arewapen sanan zan dinga turawa a paid group ga waɗan da sukayi payment. Free pages basu da yawa, guda 5 ne.... Ga Account ɗin da za'a, biya 👇🏼3108794095 Fatima Abubakar First bank Sadaidar biya 👇🏼*** "OK, kasan bana son asami akasi Ko? duk abin da ya dace kayi, shi ɗin nace muku kamar uba yake a wajena, kuma duk abin da nake musu bani da wata Manu fa face ta Alkhairi da ganin suna buƙatar Taimakon" duk kalaman nan daga wayar Abbas suke fitowa da Ogan shi yake bashi umarni."an gama sir duk yadda kace haka za'ayi babu kuskure" Abbas ya firta mai,daga bisani ya kashe wayar.Yana jinjina ma Ogan da yake ma aiki, aikin da bega ribar shi ba sai zargi in har zargin nashi ya tabbata. ****"Abdul da gaske kana son yarinyar nan?" "kai ina son ta mana so in kaji ɗaya kenan son ta da ƙunar ta nake kuma so na Aure" Abdul yaba abokin shi Faisal Amsa. "wlh Faisal Inaji a jikina yarinyar wani sashi na jiki na ce, Nifa yadda nake ji akanta abun yana ban tsoro matuƙa" "toh ka sanar mata, ni bana son Yaudara ne ta shigo duk da nasan ba halin ka bane, Amman kana ganin Ammah zata yadda?" "toh Amma nasan sai ankai Ruwa rana da ita saboda Burin ta na sai head of d house ƴa Fara Aure Kafin Nabi bayan shi" Faisal Yace "Kenan Akwai ƙura" "Bawata ƙura in Sha Allah, kawai zan fara koyama yarinyar sona Kuma alfarma ɗaya zakamin ka nema min gurbi a tahafeez ɗin su tunda kai a ɓangaren Islamiyar kake kai ni sadaƙatul jariya zan koyar Saboda ita da dan ya zama dole na fara zama malamin ta kafin, daga nan kabar min sauran Aikin nasan yadda zanyi da sauran" "ai wanan mai sauƙi ne, nasan Daktur zai baka gurbi Ai baka da matsala a addinin ka da mu'amalar ka ga sadaƙatul soyayya da zaka yi" Abdul ya kalle shi yasa dariya "au sunan da ka canja min kenan?" "a'a wasa nake ma kasan in mun haɗu dole sai mun ɗana" "Ku fa ashe HDH ne bature fa kawai a gidan ku" faisal ya faɗa yana dariya. "shima ai asali ya samo saboda indigen ɗin can da yake da shi ne tun n haihuwa, mu dake Kaga ba ƴan can bane ba a haife mu a ƙasar masu jajayen kunnuwa ba Ai mun dawo ƙasar haihuwar mu, shi ko mun yafe ma turawa shi" "yanzu da Ammah zan fara har ta bari na fara koyarwan nan Har buri na ya cika na samun soyayyar yarinyar nan" "toh ɗan gaggawa ka bari ka samu gurbin kafin" faisal y tsai da shi. "eh kuma fa haka ne, toh sai naji daga gareka, kar a ɗau lokaci abokina" Suka sa dariya, sun jima suna hira kafin suka rabu. ****"nidai duk lokacin da nayi sallah sai na ma yaron nan addu'a ni ban taɓa ganin mai RAI DA BURIN Alkhairi ba irin y...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.