FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwa Manazarciya Marubuciya Ƴar kasuwa Chocolate addict 🍫 Bookworm📗 Introvert 😚
Sample · 1
ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢTun daga nesa da su ka hangi zuwan mota ƙirar Lexus RX 350 / RX 500h, suka hangame gate ɗin Mansion da sauri, kafin isowar motocin tuni duk securities dake gate ɗin suka bayyana cikin girmamawa kowane ya mayar da kansa ya sunkuyar cike da tsoro, yana ɗaya daga cikin tsarin gidan, duk wani bawa bai isa ya haɗa ido da ɗan gidan ba sai da izini, sai kuma kallo daga nesa. Motocin na gama shiga aka rufe gate ɗin da sauri, kafin securities da sauran guards su zagaye tsadaddiyar mota acikin motocin da suka shigo, ta jima acikin motar tana amsa call batare da ta damu da wadanda ke a tsaye waje suna jiran ta acikin rana ba, yanayin fuskarta bazaka tantance murmushi take ko akasarin sa ba saboda izza dake jinin ta, tana gama wayar aka buɗe motar da sauri, guards biyu da security detail duk suna tsaye suna jiran fitowarta, nan take wurin ya ɗauki qamshin turaren ta na Dior J’adore L’Or, ta fito da qafarta dake sanye da Muaddi Heels, farare tas masu ɗauke da zanen jan lalle da suka yi matuqar fito da kyawun ƙafar, ta fito cikin nutsuwa, tana sanye da white silk shirt, da wando Burberry high-waist trousers, mai launin beige, kayan dai dai jikinta, hannunta ɗaya ɗauke da Vertu Signature Cobra ɗinta, ƙirar custom made phone da aka yi da white gold da ƙaramin ruby a gefen logo, ɗayan hannunta kuma ɗauke da Saint Laurent black tote bag, Vintage scarf ɗinta mai launin cream da ƙaramin embroidery na silver, ya lulluɓe kanta zuwa wuyanta cikin kyan ado, jan bakinta mai launin deep crimson ba qaramin kyau yayi wa fuskarta ba, idanunta boye cikin oval Dior sunglasses masu smoky lens, duk suka sunkuyar da kansu cikin girmamawa suna gaida ta, ko kallo basu ishe ta ba, qaramin tsaki taja kafin ta soma tafiyarta mai ɗaukar hankali, yanda tsinin takalmin ke bugun marbles dole qarar tafiyar ke janyo hankalin mutane zuwa gare ta, tafiya take cikin kwarewa da takalmin da kuma izza, ta na kai gab da shiga babban falon mansion aka yi saurin buɗe mata ƙofa, security na wurin suka sunkuyar da kai cikin girmamawa, ta yatsina fuska kaɗan tana kallon su, “Next time, I want that door open before my shadow touches it, bana son jira” tayi mgnr cikin sanyi da izza da wata irin muryar ta mai daɗin sauraro, duk suka amsa kusan lokaci ɗaya cikin girmamawa, ta cigaba da tafiyar ta cikin taku na jan hankali, duk suka bi bayan ta da kallo, NIHAL BILAL, ƴa guda tak a gurin Comptroller General of customs (CG) Alhaji Bilal Usman, mutum ne mai tsananin zafin kai akan aikinsa, Yana da ikon da zai iya katse kasuwanci a minti 5, ko ya buɗe wa wani masarafi ƙofa zuwa biliyoyi a cikin kwana ɗaya. Shi ya ke karɓar daily briefing akan, tariff ɗin da ake collecting a borders, seizures na contraband, high profile clearances, security risk alerts. Ko kafin ya kai wannan matsa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.