... SAƁANIN HANKALIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

... SAƁANIN HANKALI

  • 1views
  • 5chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Thriller

Loading.....Thriller Tabbas Shari'a Saɓanin hankali ce,haka kuma Shari'a mai juyin juya hali ce,tamkar saɓatta juyarta take takan ba kowa sa'a, walau mai gaskiya ko kuma akasin ta.Za ka iya ɓoye gaskiya na ɗan wani lokaci, amma ba za ka iya hana ta bayyana kanta ba na har abadaGaskiya tana iya jinkirtawa wajen fitowa,sai dai jinkirin nata ba yana nuna gazawar ta ba ne ba,don haka ko an binne gaskiya a ƙarƙashin ƙarya dubu, rana guda zata taso ta tona komi da kanta, Gaskiya bata jiran babban dalili wajen bayyana kanta,ta kanyi amfani da ko ƙaramin dalili ne,kai ko da babu dalili takan bayyana kanta,Gaskiya ba ta jin tsoron duhu domin ita karan kanta haske ce,wanda baya dusashewa a kowanne lokaci Mutum na iya gudun gaskiya, amma ba zai taɓa tsere mata ba,dole duk runtsi da tsanani ta cimma da wata rana,Haka Mutum zai iya ƙoƙarin binne gaskiya, sai dai duk ƙoƙarin da zai yi tamkar yana tono ramin binne kansa ne da kansa.Gaskiya ta kan yi shiru ne kawai na wani lokaci, amma shi kan shi shirun nata hujja ce mai ƙarfin Gaske,Ko duniya ta haɗa baki don ɓoye gaskiya, zuciya ɗaya mai tsabta zata ishe ta fallasa komiƘarya na iya gudu da sauri da sauri, amma gaskiya takan cimmata fiye da saurin da take da shi....takan riskarta cikin mafi saurin sauri,Gaskiya ba ta buƙatar kariya lokaci ne da kanshi yake kare ta,kuma ya bayyana ta da kan shi A inda gaskiya ta ɓoye, ƙarya ce ke mulki... amma kuma ba mulki na har abada ba.§§§§§§§§§§§§§§      .... SAƁANIN HANKALI    "Is that for real.... Junaid...,da gaske abinda kunnuwana suka jiye min gaskiya ne, daga bakin ka suka fito ?,...ahh...no....no".    "Oh Calm down mana Jaanam ki tsaya ki sauraren ni,kuma ki fahimce ni,Ni duk banga abun tada hankali acikin wannan zancen ba, You moved on,kin cigaba,Uhm kin kai matakin da  kike mafarki,fiye ma da yadda kike zato,So Why would you continue to stress yourself when you already have everything you need in your life?,Kina da Foundation ɗin ki na kan ki,wanda ki ke taimakon,Marayu Gajiyayyu,Masu ciwon Zuciya har ma da Masu ciwon ƙwaƙwalwa,to me zai dame ki har ya kai ga tada maki hankali iya haka ma ya isa...",Kallon da take bin shi da shine,da yanda take jan baya-baya daga inda yake ne ya sa ya dakatar da zancen da yake.      Bakin ta na rawa tace da shi,"Ya Isa....ya isa fa kace, I'm wonder,anya kuwa kaine,ka ma kuwa san me kake cewa kuwa".    Jiki a sanyaye ya kai zaune kan ɗaya daga cikin manyan-mayan kujerun da suka ƙawata Living Room ɗin,alamun ya fara gajiya da zancen ,hannayensa ya kai saman kan shi yana mai shafa shi tun daga farkon matsurar gashin kansa hi har zuwa ƙarshe,cikin ƙosawa ya sassauta muryasa tare da kira sunanta ya ce,"Shuraimah ya kamata ace ya zuwa yanzu ki yi min adalci...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “... SAƁANIN HANKALI” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play