FreeArewaPen original
FARASHIN IZZAH (Price of pride)
- 1views
- 122chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Hey there! I'm Hauwa Jibrin, aka Hauwajay writes. Anxiously waving at you! I'm a bookworm who loves reading and writing, which is why I'm here. *** journey began as a reader, and now I'm thrilled to be a writer too! A little about me: - Avid reader - Avid writer - D...
Sample · Prologue
Da gudu motar ta ƙusa kai dab da gate ɗin makarantar. Da sauri mai gadin ya miƙe daga zaunan da yake ya buɗe gate ɗin sanin motar, ya ɗaga hannu yana gaishe da wanda ke cikin motar, amma motar ba ta saurare shi ba. Wani irin 'brake' motar ta yi bayan ta isa dab da babban hall ɗin da ɗalibai suka taru don rubuta jarabawar WAEC.Buɗe ƙofar baya aka yi. Sai bayan sakanni kafin ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar. Duk hankalin ɗalibai ya koma kanta, duk da cewa idan da sabo sun riga sun saba da hakanSake sauko da ɗayan ƙafarta ta yi waje, wacce ke sanye da white socks da black expensive Toms shoes. Sannan a hankali ta fito daga motar. Sanye take da white mini hijab, white riga, da black trouser, uniform ɗin ya yi mata bala'in kyau wanda ya sake fitar da anihin kyanta, Zahra kenan 'yar shekaru 18Fuskarta na sanye da black sunglasses. Ta ɗan zaro glass ɗin daga idonta zuwa kan hancinta, tana bin wajen da kallo.Ta tashi daga jikin motar ta rufe, kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ɗan taka zuwa wajen driver. Kamar wacce aka sa dole ta yi magana, ta buɗe baki ta ce''Zaka iya jira na, dan yau ba daɗewa za mu yi ba''''Shikenan, Hajiya'' ya amsa cikin girmamawa''Hey Fatima!''Muryar ta katse nutsuwarta.A hankali ta juya, tana kallonsu har suka ƙarasoMurmushi ta yi mai ɗauke da confidence"Point of correction… Asiya" ta ce cikin sanyi"Sunana Zahra, not Fatima"Asiya da Saudat suka kalli juna suka fashe da dariya."Hey Pretty!" Saudat ta ƙaraZahra ta ɗan karkatar da kai tana murmushi ta ce"Na'am… ai a rubuce yake a fuska ta"Sai fuskar ta ɗan canza, ta koma serious ta ce"Asiya… exams card ɗina da biro?""Yana cikin jakkata" Asiya ta amsaTa gyada kaiWayarta ta fara ringing.Ta ciro ta daga aljihun wandonta ta ɗaga kiran. Kawayenta suka kalli juna cikin alamun tambayar yaushe kuma? Amma babu wanda ya san amsarSaida ta gama wayan, ta sauke daga kunnen nata"Zahra, kin canza waya ne?" Saudat ta tambayaWani murmushi mai ɗauke da izza ya bayyana a fuskar ta"Yaushe ake yayin iPhone 16 Pro… alhali har 17 ya fito?" Ta ɗan ɗaga gira"Jiya Abba ya canza min"Kawayenta suka taya ta murna.An fara kira a shiga hall.Dalibai suka fara tururuwa zuwa tantancewa don kafin shiga Hall ɗin Amma Zahra… ta kama hanyar wani office dake wani ɓangaren"Ke! Baki ganin sauran ɗalibai suna shiga hall ne?" wani sabon malami ya tsawata mataCak ta tsaya, ta juya,ta naɗe hannunta, ta gyara tsayuwartaTa kallesa kai tsaye cikin idanu cike da kwarin gwiwa."Ba zaki bi hanyar hall ɗin bane?" ya sake tambayartaA hankali ta buɗe baki, kamar waccan ake wa dole ta ce"Excuse me… kaga nayi kama da wacce zata yi exam a cikin wancan hall ɗin?With thousands of people?Babu iska… babu fanka?"Malamin ya kasa amsawa sabar shock daya shigaTa juya, ta fara tafiya cikin izzah kamar ba Malami bane ya tsayar da it...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.