FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · TURMIN DANYA
Ruwan da suka sheƙa mata ne a jikinta ya sanya ta farkawa a gigice tana sauke wata wawuyar ajiyar zuciya. Take jikinta ya hau kakkarwa kamar mazari sakamakon ruwan na da azabar sanyi ga kuma muƙu-muƙun da ake yi, sai ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye sai dai ta ji ko gezau bata yi ba domin ko ɗan yatsanta ba za ta iya motsawa ba sakamakon ɗaurin huhun goron da ta sha jikin kujerar da take kai, ta hau kici-kici amma a banza man kare. Sai lokacin ne ta shiga ƙarewa inda take kallo, kafin idanunta suka sauka a kan basamudan mutanen da suke tsaye ƙiƙam a kanta sun zubo mata maganansu, dukkan su sun murtuƙe fuska tamkar magribar ɗinya babu alamun ɗigon imani a tattare da su. Sai lokacin ƙwaƙwalwarta ta shiga dawo mata da dalilin wanzuwarta a wurin daki-daki. Ta runtse idanunta da ƙarfi. 'Tabbas na san dama a rina an saci zanin mahaukaciya, amma alƙawari ne na ɗauka wa kaina kuma duk wu...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.