FARGAR JAJIFree

ArewaPen original

General fictionFreeCompleted

FARGAR JAJI

  • 1views
  • 22chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · ƊANƊANO.

*Friday, 10 April 2026**DAGA MARUBUCIYAR.**TA FITA ZAKKA**GIDANMU**KANA NAKA**TSAKA MAI WUYA**IDAN AN CIZA**TURKEN GIDA**JANAFTY*❤️*AREWABOOKS:JamilaUmarJanafty*.****:JamilaUmar315**** DAGA LITTAFIN FARGAR JAJI.*Sannu da zuwa Noori."Ta faɗa tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a ɗakune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe ɗazu to a yanzu ma haka ya shigo Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau.Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa."Noori."  Ta faɗa cikin sanyi da karyewan murya.Sai da ya sha ruwan rabin goran  sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki."Ga abinci."Ta faɗa tana nuna masa Dinner ɗin da ta gama shirya masa komai tun ɗazu."Na ƙoshi."Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi  a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba.Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya  a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi."Noori."Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a."Me ya faru ne? Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa.Sai ta yi mirmishi kafin ta ce."Wai akan mganar ciki ne?Ga mamakin ta  sai ya amsa mata da cewa."E."Ta ɗauka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faɗa masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba."To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba."Har ta gama mgana bai ɗago ba, yana cigaba da latsa wayarsa."Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni."Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi."Am sorry Noori na. Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni?Ta faɗa tana mai kwantar da kanta a saman kafaɗan shi.Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters22
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play