FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
⚖️TUHUMAH.⚖️🥰 MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*Bismillahirrahmanirrahim.**Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, Allah ina roƙon Ka ka sa yadda na fara rubuta labarin nan lafiya na kammala shi cikin aminci da ƙoshin lafiya.* PAGE 1️⃣Cikin hanzari yake tafiya da kamar zai tashi sama, kyakykyawan matashin saurayine, wanda a ƙalla zai kai shekara ashirin da takwas zuwa da tara. Sanye yake cikin riga da wando na makanike, a kafaɗar shi rataye da wata ƴar jaka duk ta ɓaci da baƙin mai, da alama daga aiki ya taso. Sai da na masa kallon tsaf na gano baiwar zallar kyau da cikakkiyar haiba da Ubangiji ya masa. Fatar shi baƙa ce sai dai ba baƙi irin sosai ɗin nan ba, baƙi ne mai kyau irin sheƙin nan.Kyakykyawar zagayayyiyar fuskar shi ɗauke take da manyan idanuwa dara-dara, yayin da launin idanun suka kasance farare tas ƙwayar cikin su kuma baƙa siɗik. Yana da zara-zaran gashin ido yadda kuka san na mace, sai kwantacciyar girar shi wadda take a cike har haɗewa ta yi da ƴar uwar ta. Yana da dogon hanci Masha Allah Ƙasan hancin ɗauke yake da ɗan madaidaicin bakin shi wanda kalar laɓɓan suka kasance masu ɗan duhu.Yana da yalwar sumar kai duk da ya yi aski irin saisayen nan, amma kallo ɗaya za ka wa kan shi ka gane yana da cikar suma sakamakon yadda gashin kan nashi yake a kwance tamkar na Fulani.Ƙarar horn ɗin da aka danna ne yasa ya ƙara saurin tafiyar shi, Ganin motar tasha gaban shi hakan yasa ya tsaya tare da sa hannu ya dafe goshin shi, ya zubawa motar ido ya jan tsaki yana jin ran shi babu daɗi.Buɗe murfin motar aka yi wata kyakkyawar mashiyar budurwa ta fito, a ƙalla zata kai shekara ashirin, fatar ta fara ce irin farin nan mai ɗaukar hankali, sanye take cikin doguwar rigar abaya baƙa, daga gaban rigar an mata kwalliyar golden color, Sam ba ta da jiki irin siririyar nan ce, sai dai tana ɗan cika daga ƙasa.Yana ganin ta fito ya ja tsaki tare da fara tafiya dan barin wajen, tana ganin haka da sauri ta sha gaban shi, ta narke fuska tare da haɗa hannayen ta duka biyu alamar roƙo ta ce"Dan girman Allah Ya Anwar ka tsaya ka saurareni."Haɗe fuska ya yi babu alamar wasa yace "Bani hanya na wuce." Ganin babu wasa a fuskar shi, hakan yasa ta matsawa ya wuce.Da sauri ta bishi a baya murya na rawa tace "Ka tsaya mu yi magana dan Allah.""Banda sauran magana dake Hafsat." Shima ya faɗi hakan, yana daɗa saurin tafiyar shi.Ganin za su shiga cikin mutane, sai ta yi saurin shan gaban shi ta narke fuska, tare da haɗe hannayen ta biyu alamar roƙo, hakan yasa ya dakata daga tafiyar da yake, ya ɗago ya watsa mata idanun sa dake da wani irin kwarjini cikin dakakkiyar murya yace"Hafsat ki bani hanya na wuce."Duk da yanayin nashi ya ɗan tsorata ta, domin ba ta taɓa ganin...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.