FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Ina alfahari da kasancewata marubuciya
Sample · Chapter 1-2
SALON ƘISSA(Love & Romantic story) 💋❥💋❥💋 Mom IslamPage 1-2Horn ya danna a ƙofar wani tangamemen get baƙi mai kyau, mai gadi ya buɗe musu get ɗin, Alhaji Ibrahim ya kutsa hancin motar cikin gidan, a parking space ya ajiye motar, kana ya buɗe murfin mota ya fito, Raudah dake ɓangarensa na mazaunin Driver ta buɗe itama ta fito, Hajiya dake zaune a backside tayi tsuru-tsuru da idanu, dan bata san ta yaya zata bude murfin motar Ba, magana take tana daga ciki amma basa jinta, kasancewar glass ɗin a rufe yake,Ibrahim ya ɗan matsa tare da bude murfin motar kana yace "sannu Hajiya ansha hanya"Hajiya ta wani yamutsa fuska da ƴar lalitarta a hannu da kuma jaka a rataye a wuyanta irin wacce ake saka waya a ciki, "Ni bafa zan juri wulaƙanci irin na ƴan binni ba, cikina yana ƙugi yunwa nakeji ace daga ƙauye zuwa Kano baza'a siyawa mutum komai ba dan mugunta?"Raudah ta ƙunshe dariyarta, ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.