FreeArewaPen original
RAYUWAR DA NA ZAƁA
- 1views
- 8chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Alƙalami ya fi takobi🖊️📝
Sample · Part 01
RAYUWAR DA NA ZAƁAPart 01... Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.“Ke wai Maryam yaushe za ki gusa ki ba mu guri? Kullum kina makale a cikin ɗaki, kamar wata bokanya. Dubi kawayenki ki gani, duk sun yi aurensu, wasu ma daga cikinsu har ƴaƴansu. Amma ke kullum kina zaune a gida, abin ko damunki ba ya yi." Muryar Inna ce take dukan kunnena kamar saukar aradu. Na ja dogon numfashi, idanuwana suka cika da kwalla, na kasa cewa uffan. Ina zaune a gefen gadona, na lumshe ido ina jin yadda ɗacin kalaman da Inna take furta min yake ratsa zuciyata.“Inna, don Allah ki yi hakuri. Shi aure ai lokaci ne, idan lokacin ya yi ai zan yi.” Na faɗa da muryar da take rawa, ina kokarin danne kukan da yake neman kubuce min.“Wane lokaci kuma Maryam? Shekararki talatin fa! Talatin fa Maryam! Har yaushe ne lokacin nan zai yi? Idan kina tunanin karatu ko aikin office ne ya hana ki aure, akwai mata d...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.