FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · TURMIN DANYA
TURMIN DINYA NAFATIMA UMAR KAS(Mummyn Mihal)(7)A lokacin da suka jefa ta motar figarta suka yi da gudu suka bar wurin, fizge-fizge take yi tana dukan motar da ƙarfi tana faɗin "Ina za ku kai ni? Ku buɗe mini mota na fita, wayyo Allah ɓarayi." Mari na kusa da ita ya zuba mata. Duk da haka ta cigaba da ƙoƙarin kai hannu domin ta buɗe motar amma ta kasa, wani marin aka kuma zuba mata sannan ya buga mata tsawa kan ta yi musu shiru. A tsakiyar su suka saka ta, ɗan kwalin kan ta ɗaya ya fizge ya ɗaure mata ido da shi, bayan ɗayan ya riƙe mata hannuwa ta baya tamau, sam ta kasa motsi sai bakinta da ya ƙi shiru tana ihun kiran taimako. Sai dai babu wanda zai ji ta kasancewar motar a ɓame take kuma gilasanta masu duhu ne Tun tana ƙoƙarin ƙwatar kanta har ta haƙura domin ta galabaita. Sun ci tafiya sosai kafin suka iso sansaninsu. Tsayar da...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.