FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · TURMIN DANYA
TURMIN DINYA NAFATIMA UMAR KAS(Mummyn Mihal)(11)Wata wawiyar ajiyar zuciya Daddyn ya sauke yana samun wuri ya zauna sannan idon shi a kan su ya ce "Zazzaɓi ne ya mata kamun kazar kuku sakamakon cizon da sauraye suka yi mata, sai ciwon kai. Raunin goshinta kuma ina tunanin faɗuwa ta yi ko ta buge saboda idanunta a rufe suke haka hannayenta." Ta hau girgiza kai idanunta a kan ta kafin ta ce "Yanzu sai yaushe suka ce za ta farka?""Eh to a kowanne lokaci ma za ta iya farkawa. Ni bari na je na dawo tunda kin zo, ki kula da ita." Kai ta gyaɗa tana neman wuri ta zauna shi kuma ya fice. Nuran ya ƙaraso ya sauke jakar kafaɗarsa ya zauna a bakin gadon shi ma duk suna jiran farkawarta. Sai can yamma sannan ta farka, ji ta yi kan ta ya mata nauyi "Sannu Nuratu" Suka haɗa baki wurin faɗa. Kai ta gyaɗa tana dafe kan ta da ke sara mata. Kama ta ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.