KISHIYAR WAJEFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

KISHIYAR WAJE

  • 1views
  • 11chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

KISHIYAR WAJE 1SADIYA GARBA YAKASAIDigon hawaye babu a fuskarta duk irin bugun da ta ci agun sa bai sa zuciyar ta rissuna ba,yakan sha mamaki in ya ga yarda take shanye dukan da yake mata da zarar ta masa laifi,kuma bakin ta ba ya mutuwa sannan bata san tace yi hakuri ba,ko da kuwa zai kwana yana dukan ta.Tausayin ta ne ya kamashi ganin jini na fita ta gefen goshin ta kuma bata yi kokarin tarewa ba,da kansa ya ajiye dankon da ya dake ta da shi ya shiga kitchen in da yake ajiye first aid din sa ya fito ya sa mata ido ta takure akasa tabar kan kafet din da ya tattare saboda yawon da suka sha na buyar kar ya buge ta.Rashin kyautatawar sa yake gani me yasa yake dukan macen da yake so?ya cije leben sa yana jin kaman ya yanke hannayen sa da suka doke ta,yasan hakan ba zai yi ba amma saboda Allah me yasa bata jin maganar sa.  Matso na gyara miki sai kije ki yi wanka ki sha shayi ga magani ki sha.Ta dan cije lebe takaicin sa ke ci mata rai kwarai da gaske wannan ba so ba ne cin zali ne ba kuma zata kuma daukan cin mutuncin ta da yake yi ko da yaushe.Mikewa tayi da kyar da yake fara ce shayin bulala kwance a jikin ta shi da kansa ya tsorata da ganin aika -aikan da yayi.da kyar take takawa ya mike jiki ba kwari ya sha gaban ta ina za ki?Wata harara da ta zuba masa sai da ya ja baya ,ta cigaba da tafiya bai fasa bin ta ba ya kamo hannun ta da zafin nama ta fincike hannun ta ta watsa masa harara gami da nuna shi da yatsan ta kar ka sake tabani abu mafi daraja tsakanin mu ka fita cikin gidan nan.Ya murtuke gami da tunkarar ta bata matsa ba amma tana jin zata iya da shi,ya murde mata hannu gami da hada ta da garu ba ki isa na fada ki musa mun ba,ta limshe ido saboda zafin matsa amma ta girgije tace saboda kai ubana ne ko kuma kai ka halicce ni?Ya dan rangwanta mata kadan yace saboda ni na ajiye ki zamana kike ,ta dan yi murmushi zaman wahala zaman rashin 'yanci to bari ka ji zaman DADIRO ba zaman aure ba ne ka saurare ni da kyau zama ne na yarda ka na so na ina son ka zamane na rasyi ba addini ba kuma zama ne na sabon Allah to na daina.Ba ki isa ba marar kunyar banza,ni na ajiye ki na baki gida,ci da sha da suttura don haka ni ke da iko da ke.Dariya ta saki tace ji ka ko kunya baka ji ba ks ajiye ni kana zalunta ka adana matar ka a gida ni kana zaman munafunci da ni to na daina baka da ikon yi min dole wallahi.Na isa kuwa yarinya har nayi yawa kin san ni waye ai don haka ki kama kan ki ni na isa na bar ki ba ke ki ka isa ba don haka ki bi ni a hankali.Yayi jifa da ita kan kujera bayan ta yayi kara ta runtse ido tana kin radafin ciwo ya biyo ta ya taushe ya gyara mata ciwon ta tsiya tayi mukus ta kasa tabukaws saboda bata da karfin ramawa in ta zafafa za tai ta shan wuya a banza.Da kansa ya ksita bandakin ya ja mata kofa ta fada kwamin wanka tana g...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters11
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play