HAULA HABEEBFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

HAULA HABEEB

  • 1views
  • 18chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · BABI NA ƊAYA.

   💎🌹Haula Habeeb 🌹💎2026 Edition        By Amdeey Tejj d'Unique. Gargaɗi Ba a yarda wani, wata ko wasu gungun mutane su yi amfani da wani ɓangare na wannan littafi ba ta kowace hanya face sai da izinin marubucin. Yin hakan babban laifi ne da ke iya kai mutum ga shiga komar hukuma. A kiyaye. Jan Hankali Wannan labari ƙiƙirarre ne. Ban rubuta shi don cin zarafi ko tona asirin kowa ba. Duk wanda ya ga wani abu da ya yi daidai da rayuwar shi, to ya sani arashi ne ba da nufi ne ba. Jinjina Jinjina ta musamman ga ɗaukacin membobin Future Writers Association (FUWA) The Rising Star Team. Allah Ya bar zumunci kuma ya ƙara hazaƙa. Bismillahir Rahmanir Raheem.   *HAULA HABEEB*         BY AMDEEY TEJJ D'UNIQUE BABI NA 01A wayewar garin yau, wadda ta kasance ranar Asabar, daidai da sha takwas ga watan Maris ne ake sa ran wayewar garin da za ta zo wa ahalin gidan da wani irin farinciki na musamman sakamakon abin alherin  da za a ƙulla a cikinsa. Sai dai kash! Saɓanin hakan ne ya faru, maimakon farinciki sai ma baƙinciki da ya maye gurbinsa, hakan kuma ya faru ne sakamakon mutuwar ɗaya daga cikin waɗanda za su zama silar ƙulluwar wannan farinciki.Motoci ne a jere  tun daga harabar gidan har waje, kowa idan ka kalli fuskarsa sai jimami yake yi tare da jinjina kai bisa irin wannan iko da ƙudira irin wadda Ubangiji mai yin yadda Ya so, a sa'adda Ya so, ba tare da wani ya tuhume shi dalilin yin hakan ba Ya nuna. To, idan ba haka ba, wa zai ma haka kuma ka yarda? Ai sai dai Shi ɗin mai iko da kowa da komai. Mai cewa kasance kuma ta kasance, ba yadda ka iya ko da ba yadda ka so bane, wato Allah maɗaukakin sarki kenan.Daga cikin gidan kuwa ban da koke-koken mata ba abinda ke tashi, wasu kuma sai aikin lallashi suke yi, zuciyoyi da yawa sun yi ƙunci babu daɗi, amma duk da haka a wani ɓangare na gidan kuma wasu zuciyoyin cike suke  farinciki tamkar an yi musu babban albishir.A can cikin babban falon gidan, wata mata ce zaune a kan kujera sai kuka take yi, ta ma kasa magana, mutane sai baki suke ba ta, bisa ga dukkan alamu dai ita ce mahaifiyar wadda ta rasun. A zahiri mutuwar kawai take yi wa kuka, amma a baɗini akwai wani ɓoyayyen dalili a bayan wannan kukan. Ana cikin wannan hali ne aka fito da gawar za a kaita makwancinta. Wata daga gefen matar ce ta ce, "Yaya na yi juyin duniya da ke kan ki je ki yi mata addu'a amma kin ƙi, ga shi har za a fitar da ita. Don Allah ki ƙarfafi zuciyarki, shi fa dama mai rai mamaci ne. Allahn da Ya ba mu ita, yau karɓi baiwarSa. Kuma kin san cewa Ya fi mu sonta. Addu'ar samun rahama da dacewa a makwancinta ya kamata mu yi mata. Don Allah ki daure.''Ba ta motsa ma balle ta sa ran za ta yi abin da...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters18
premium8
11

BABI NA GOMA SHA ƊAYA

Premium
Updated 4 months agoAvailable now
12

BABI NA GOMA SHA BIYU

Premium
Updated 4 months agoAvailable now
13

BABI NA GOMA SHA UKU

Premium
Updated 18 days agoAvailable now
14

BABI NA GOMA SHA HUƊU

Premium
Updated 4 months agoAvailable now
15

BABI NA GOMA SHA BIYAR

Premium
Updated 18 days agoAvailable now
16

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Premium
Updated 4 months agoAvailable now
17

BABI NA GOMA BAKWAI

Premium
Updated 4 months agoAvailable now
18

The Closed and The Opening Door.

Premium
Updated 4 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play