GANGAR DUHU!Free

ArewaPen original

ActionFreeCompleted

GANGAR DUHU!

  • 1views
  • 68chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

GANGAR DUHU!‏Gargaɗi:wannan littafin ba na yara bane🔞, If you know you’ll end up insulting me, it’s better you don’t read it kawai ki ƙara gaba saboda book ɗina na masu hankaline😉.Zm~Chubaɗo✍️‏بسم الله الرحمن الرحيم  Page: 1Garin Kano cikin Unguwar Zage da misalin ƙarfe 1:pm na rana. Gidane mai matsakaicin girma da ga kallon farko zaka fahimci cewa gidan Gandu ne. Ɗakunan dake cikin gidan guda huɗu ne kuma ko wanne ɗaki ciki da falo ne, babban abinda zai baka mamaki shine kowa harkar gabansa ya keyi bame shiga harkar kowa, ma'ana duk abinda kaga dama shi za kayi ba mai taka maka birki.Gabaɗaya matan dake rayuwa a cikin gidan duk yaran matane ma'ana duk matasa ne ba masu yawan shekaru na azo a gani ba. Mutum ɗayace mai shekaru da yawa ita ce Baba Atine, wadda ba zata wuce shekaru sittin da biyu a duniya ba. Kowa hada-hadar gabansa ya keyi masu yin wanke-wanke nayi hakama masu yin saƙar hannu sunayi, kamar daga sama suka fara jiyo hayaniya da kuwar jama'a daga ƙofar gida, malam Bello Mijin Sahura ne kawai a gidan Amma Mijin Bintalo da Abuwa duk sun fita neman sisin kwabo.Taɓe baki Bintalo wadda ke zaune akan kujera ƴar tsuguno ta yi, sannan ta kalli Abuwa dake saƙa a ƙofar ɗakinta ta ce,"Kai Allah ya sauwaƙe wllh, ni dai da haihuwar mutumin banza irin wannan yaron wllh gwara na koma ga Allah ban haihu ba. Wannan wace irin masiface saboda Allag? gabaɗaya yaro ya zame mana bala'i a cikin Gida." dariya Abuwa ta saki tareda Ajiya zaren saƙar dake naɗe a hannunta ta ce,"wllh kamar kin shiga raina kin leƙa, ke nifa na gama gajiya da bala'in da wannan ɗan iskan yaron yake jefa mazajanmu." ta faɗa tana riƙe haɓa tana kallon Bintalo wadda ke ƙoƙarin juye taliyar ƴar mirjin  da ta ɗora a wuta. tsaki Bitalo ta ja mai ƙara tareda ɗibar ruwa a farin bokitin dake ƙofar ɗakinta ta ce,"don bala'i da masifa kullum gidan mu a zagaye yake da ƴan-sanda sai kace gidan ɓarayi? ni dama wataran su kashe ɗan iska a karanbatta kowa ya hut......" "Hmmm Bintalo kenan, to  meye marabar Ɗandaba da ɓarawo?" Abuwa ta jefa mata tambayar yayinda take kallonta cikin ido. "Hakane wllh babu wata maraba tsakaninsu duk kanwar ja ce, duk inda ɗan sara suka yake to baka rabashi da satar kayan jama'a." cewar Bintalo. "Wai Bintalo mai yasa bakinku baya faɗar alheri ne?" Baba Atine ta faɗi haka yayinda take yaye labulan ƙofar ɗakinta ta fito tana kallonsu, sannan tacigaba da cewa,"wllh kuna bani mamaki ku biyun nan idan ku ka aikata wani abin sai naga kamar baku san zafin haihuwa ba." kallon galala suke binta dashi ba tareda sunyi magana ba. murmushi Baba Atine tayi mai sauti sannan taci gaba da cewa,"ga dukkan alamu  baku san haihuwa ba'ai mata zaɓe ba shiyasa kuke faɗar duk abinda yazo bakinku akan ƴaƴan wasu, amma ba komai Allah ya bamu...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “GANGAR DUHU!” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play