FreeArewaPen original
SARA DA SASSAKA...
- 1views
- 71chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Simple minded
Sample · CHAPTER 1
SARA SA SASSAƘA...AISHA ADAM (AYSHERCOOL)YOUNG TALENTED WRITE'S ASSOCIATION (YOTA 002)BRIGHT PENS.ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YI SHI DOMIN CIN ZARAFI GA WANI KO WATA, HUKUMA KO MAKAMANCIN HAKA BA. IDAN YA YI KAMANCECENIYA DA RAYUWAR WANI, KO KUMA WANI ABU MAI KAMA DA HAKA. ARASHI NE, DUBA DA YANAYIN DA MUKE CIKI NA RASHIN TSARO, HANKALI YA RAJA'A GURIN AMFANI DA HANYOYIN NISHAƊI KAMAR FILM DS LIATTAFAI DOMIN ƘARA SANAR DA DUNIYA HALIN DA YANKINMU YAKE CIKI. SABODA HAKA IDAN YA YI KAMANCECENIYA DA WANI ABU ARASHI NE.NA FARA RUBUTUN LABARIN 6/1/2026 NA FARA POSTING 27/5/2026BAN YARDA A JUYA LITTAFINA TA KOWACE FUSKA BA SAI DA IZNINA.BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIMP115 ga watan Ogusta, hadari ya yi ganganko a sararin samaniya, babu abin da ake iya gani face hasken walƙiyyar da hadarin yake ta yi babu ƙaƙƙautawa. Haka zalika babu abin da kunnuwa ke iya ji, banda sautin rugugin cidar hadarin nan.Riƙe yake da hannun matashin yaron da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma riƙe da kaya, su na ta sauri, suna ratsa tsakanin zangarniyar hatsi, da ta yi tsawo, kasancewar tsakiyar damuna ne, amfanin gona ya fito ya yi kyau.Da kyar yaron yake cira ƙafafuwansa, duk da saurin da mutumin da ya riƙa masa hannu yake yi.Zuciyarsa ɗauke da wani nauyi da yake barazana ga numfashinsa, haka yake bin mutumin, yana jin kansa tamkar ba shi ba. Sannu a hankali yayyafi ya fara sauka kaɗan-kaɗan, a daidai lokacin da walƙiyya ta haska wata ragargajajjiyar hanya mai tarin kwazazzabai da da ramuka suka fito.Mutumin ya kalli yaron, zuciyarsa na wani irin raɗaɗi, tamkar mai ci da wuta, raɗaɗin da yake tasowa daga zuciyarsa har maƙogwaronsa yake ji, tamkar zai tsage,ya ja ya tsaya.A raunane ya dubi yaron ya ce "Ka yi haƙuri, tun da na fito da kai hanya, maza ka yi sauri ka bar garin nan, kar ka bari gari ya waye su cim maka, ka dai ji abin da suka faɗa da kunnenka. Idan Allah ya ƙaddara saduwarmu a gaba, sai mu sake haɗuwa.Ya damƙawa yaron ƙullin kayansa, sannan ya zura hannunsa a cikin aljihunsa, ya ciro kuɗi ya damƙa masa."Ga wannan, maza ka ci gaba da tafiya, idan ka samu guri ka laɓe kar ruwa ya dake ka"Tun da ya fara maganar, yaron yake bin idanunsa da kallo ta cikin hasken walƙiyar da ake yi.Jikinsa a sanyaye ya ce "Ka tafi sumale, kar su same ka" Ba tare da ya furta uffan ba, yaron ya juya ya fara takawa, bai fi taku biyar ya yi ba, ya tsaya ya waiwaya, ya ga mutumin ya kama hanyar komawa cikin ƙauyen. Ya tsaya ya zuba masa ido, a dai-dai lokacin da ruwa mai ƙarfin gaske ya ɓalle, ya fara zuba a jikinsa."Zan dawo, tabbas zan dawo, gobe, jibi, ko kuma gata? Ban sani ba, amma dai na san zan dawo" Ya furta yana haɗiye wani raɗaɗi da yake yi masa ɗaci a maƙogwaronsa.*****Gari ya yi tsit, babu abin da ke tashi, sai sautin kai komon ababen hawan jami'an tsaro, tituna babu kowa sakamakon dokar ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.