FreeArewaPen original
HALIN YAU!
- 1views
- 13chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
🌺 *HALIN YAU*! 🌺*Lafazi writer's association*.*Bojuwa herbs**By**Surayya Dee.*****.**Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.**Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.**Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.**Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.**Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.**Akwai packages na mussaman ga Amare, uwayen gida, zawarawa da masu jego.**Tuntubeta a wannan lambar*******Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.**Bismillahir Rahmanir Rahim**Ina farawa da sunan Allah, ina neman tsari da rubuta 'Barna! Ina rokon na yi rubutun da za'a 'karu , ayi amfani da shi.Tsira da aminci ga shugaba Annabi(S.A.W.).* *GARGADI*_A kiyayi taba min labari na ta kowacce siga, Hakkin mallakar tawa ce ni ka'dai, Dole sai da izinina kafin a karanta shi a kowacce irin kafar sadarwa, wadda ya shiga hakkin mallaka kuma ubangiji ya isar mini._ *JAN KUNNE* *Gaba'daya Wannan labarin kirkirarsa aka yi(Fiction)!haka sunaye da garuruwan da ke ciki bana kowa bane, na zabe sune kawai dan 'kawata labarin, dan haka duk wadda yaci karo da abin da ya yi kamacanceceniya da rayuwar sa bada shi ake ba, arashi ne kawai* *JINJINA*_GA MARUBUCIYA_*FADILA LAMIDO**SUGARI BA KI YI FARIN BANZA BA*. *SADAUKARWA*_Tun daga farkon labarin har zuwa karshen sa gaba'daya sadaukawa ne ga shugaban kungiyar_ *LAFAZEE WRITERS**SADIQ ABUBAKAR*. 1-2Harabar makarantar kwana ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kiyawa (FGC Kiyawa), cike take mak'il da motoci da jama'a kama daga iyayen yara, da su kansu daliban rukuni-rukuni, gungu-gungu, cike da walwala sai ciye-ciye ake yi kasancewar yau ake ziyarar dalibai (visiting day).Daga can gefen lambun makarantar, wata matashiyar uwa ce da a 'kalla ba za ta wuce shekaru talatin da biyu ba. Zaune take kan lallausar darduma wacce da alamu da ita ta zo, gefenta kulolin abinci ne da kuma ledoji masu dauke da tambarin *Sahad Store.*Zaune take tana baza ido ta ga ta ina tilon dan'ta zai bullo, ba ta ankara ba ta ji an rungume ta tare da ambaton "Mamiii!"Cike da dariya ta dago kai."Jawad wai ba ka san ka girma ba ne? ba don a zaune nake ba ai da ka kayar da ni." Ya sake komawa ya kwanta a jikinta tare da cewa,"Nayi kewarki Mami! Ina Inna?"."Ta ce, a gaishe ka, shekaranjiya ta tafi Gamawa biki""Ki ce ba ta yi mini girebar ba kenan?" Ya fada cikin turo baki irin na sakalan yara."Wace ita? Ai ranar Laraba yini ta yi tana hidimar girebarka, bata samu sukuni ba sai da ta kammala."Sai a lokacin ya saki fuskar yana cewa,"Al...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.