FreeArewaPen original
BAƘON YANAYI
- 1views
- 16chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm Ishaq Nasir Abdullahi also Known as Nasrullah Writer And also a reader
Sample · PAGE 1
________________Maimunatu ce tafe kan hanya ta fito bakin layin unguwarsu, wurin shagunan bakin unguwa haka. Domin samun abinda zata saka a bakin salati, sanmakon da tayi shine yasa ta fito da wuri tunda wasu masu shagunan ma basu bude shagunansu ba, wuri ta samu ta zauna tana jiran zuwansu, lokacin da 7:30 na safe tayi sai gashi sun fito kowa yana buɗe shagonshi, Maimunatu baiwar Allah ba kowa take jiran buɗe shagonshi ba face Alh Musa Mai kanti baki layinsu, ko da ganin zuwanshi ya buɗe shago Maimunatu wani sanyi taji a cikin zuciyarta, tashi tayi tana faɗin, "Bismillahi" kai tsaye shagon ta nufa.Tana zuwa bakin kofar shagon tayi masa sallama "Assalamu alaikum" ya amsa mata da, "Ameen Wslm" sanan ya kara mata da sannu da zuwa ya cigaba da fadin, "Kece haka tun farar safiya?" Ko da jin hka cikin fara'a ta amsa da, "Eh zuwana kenan na hango shagunan naku duk a rufe suke shiyasa na samu wuri can na tsaya domin ganin fitowarku Alhamdulillah, cikin abunda bai wuce rabin sa'a ba sai gashi kun fito" "Allah sarki ina ce dai duk gidan lafiya?""Eh Alhamdulillah, amma kasan abunda ke tafe dani""Mekenan Malama Maimunatu?""Alhamdulillah da sauki, Alh Musa nazo ne a sake taimaka mana kamar yadda aka saba mana da can"Ko da jin wannan furuci nata Alh Musa Hade rai yayi yana faɗin,"Eh tom gaskiya ni kam yanzu nayi iya abunda zan iya gaskiya indai maganar wani bada kaya ne, ko wani bashi tsakanina daku yanzu gaskiya babu shi, saboda wanda akai ma na bayan baku biyani ba, saboda haka ba zan sake kara baku wani bashin ba ina mai baki haƙurin hakan kuyi hakuri dan Allah!"Ko da jin haka bata sake cewa komai ba, duk jikinta mutuwa ya yi kamar an mata duka ta rasa abinda ke mata daɗi.Bata san lokacin da fito daga cikin shagon Alh Musa ba, can ta kara gaba wani shago wanda ake kirashi Sani Master, ko da zuwanta sallama tayi masa ya amsa tayi Sa'a shagon nashi ba mutane aciki daga ita sai shi shagonsa babban shago ne shima domin komai yaji acikin shagon ne Allah ya rufa masa asiri, cikin fuska mai dauke da murmushi mai narkar da zuciya ya fara mata mgana,"Sannu da zuwa tawan oyoyoyo lale maraba"Ko da jin haka kallon shi tayi ta watsa masa harara tayi taja tsaki Mtswww tana fadin,"Innalillahi menene haka?"" Kamarya innalillahi sai kace kinga wani mugun abu? Kuma sai kace ke ba yar gari ba? Haba mana ki zama wise mana"Ko da jin haka sake kallonshi tayi, tana cewa,"Astagafirullah Allah na tuba, wallahi kullum addu'a nake Ubangiji Allah Ya hanani mugun gani mugun ji da sharri mutanan banza mtsww"Ko da jin wannan furuci Sani Master Hade rai yayi yana fadin," Okay dakyau meke tafe dake?"Cikin muryar van tausayi tana fadin,"Dan Allah ka taimaka mana, na sake dawowa wurinka ne badan komai ba sai dan ka taimaka mana dan Allah kuma ina son ka manta da duk abunda ya faru ab...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.