FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chaptee 1
*Gargada* Na Ikilima Adam Ina mika sakon gaisuwa da fatan alkhairi da yan uwa da abokan arziiki na.Duk wani alkairi dake cikin wanna littafin Allah ka bani ladansa akasin haka , Allah ka yafe min. Littafin nan ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba.Kuma ban yarda ayi amfani dashi ba , babu izinina ba .Littafin kudi ne akan naira 700 kacal zaki sha karatunki bayan gama sakin free page.Bismillahi rahmanin rahim Page 01Shari'ar da ake gudanarwa a kotu, wadda gidajen talabijin ke haskawa har da tashar canal 3 , sharia ce mai tashin hankali inda aka gurfanar da wata yarinya yar shekara sha biyar.A gidan Alhaji Abdullahi, sosai iyalan gidan hankulansu ya karkata wajen kallon wannan sharia da ake gudanarwa tsakanin matar attajirin da aka kashe , da kuma wannan yarinyar yar shekara sha biyar .Alhaji Abdullahi dake zaune kan kujerarsa ta alfarma ,gefensa matarasa ce da yayansa da dukansu hankalinsu na kan wannan shari'ar." Alhaji yanzu yara kanana suke kisa , daga masu kashe mazan su don kishi, sai masu kashe maza dan kwadayi , yanzu duba wannan yar cokalin yarinyar wacce autarka ma ta girmeta wai ita ce ta kashe uban gidanta" sai ta numfasa tana mai kallon Alhaji Abdullahi dake jinjinawa da kai hakan yasa shi fadin." Amma kuma kaga yarinyar nan wallahi kamar ba zata aikata ba , yarinya karama daga ganinta bata ma gama mallakar hankalin kanta ba , kuma sai nake ganin kamar ba zata iya kashe bera ba bare har ta kashe mutum , don dai ance mugu bai da kama da sai ince akwai lauje cikin nadi" sai yayi shiru yana jin yarsa me shekara 18 na fadin ." Dad ni dai don Allah ka taimaka mata , ko tayi kisan nan yarinya ce fa " shiru tayi ganin isowar babban yayansu a falo .Sanye yake cikin shadda fara sol mai sheki .kallo na masa na tabbatar Allah ya nuna ikonsa a wurin halittarsa. fari ne sol tamkar zubin larabawa, tsaye yake , dogon namiji ne wanda bashi da kiba , sannan ba za'a sashi jerin ramammu ba , jajjayen labansa ba karamin kyau suka kara masa ba , zanen hancinsa ya tafi cif-cif . Agogon hannunsa yake kallo yana mai durkushe har kasa gaishe da mahaifinsa da matar ubansa dake kusa dashi . Kannensa mata ukun dake wajen duk sai da suka gaishe shi , amsa musu yake cikin cool voice dinsa.Idanunsa ya kai kan talabijin akan sharia da ake yi , kana ya dauke idanunsa yana mai fadin." Dad , yau zanyi saurin fita, daga cen zani sallah juma'a " yayi magana ne yana kokarin barin falon." To Assadiq Allah ya kaika lafiya " cewar Alhaji Abdullahi da kannensa .matar uban nasa Hajiya Rahma cike da jin dadi ta furta." Gaskiya Assadiq yaron nan akwai ladabi , Allah ka bashi mace ta gari , shi da kaninsa Ahmed"."Ameen " cewar Alhaji cikin jin dadi . Kana yana kallon yanda yaran suke kallon wannan sha...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.