RAGAYAR DUTSEFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

RAGAYAR DUTSE

  • 1views
  • 28chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writing is my passion❤️😍

More from @nanahaleema11

Sample · Official thriller

*RAGAYAR DUTSE.* *Nana Haleema* *Official Thriller* *A 2026 Novel.* *Daga marubuciyar, KWANTAN ƁAUNA, BAYA DA ƘURA, KIRAN RABO, MAI ƊAKI....* *** "Are you out of your mind? Duk bathrooms ɗin da suke apartment ɗin nan, you could'nt find one to use except the public one in the main palour?. What kind of nonsense is this?." Islaha ta ɗago ta kalle sa jin yadda yake yi mata magana cikin kaushi da zafi, bata taɓa jin muryarsa a haka ba, bata taɓa ji ya yi magana mai ƙarfin wannan ba. Ko yaushe magana yake yi cikin steeze, yana yi yana basarwa. Amma yau ta ji akasin haka, har yana shouting. Bata motsa daga inda take ba, duk kunya ta gama mamaye mata idanunta ta ce, "don Allah ka bani waje in shirya, bana so kana shigowa inda nake  anyhow. Ka san dai ni ba muharramar ka bace, zuwa inda nake without permission haram ne." Tsabar takaici bai san ya riƙo hannunta ya miƙar da ita tsaye ba. Bata yi zato ba zai yi hakan ba ko kaɗan, ta yi saurin riƙe towel ɗin jikinta, jin zai kwance. Ya ce, "baki ji me na ce miki ba? Ina yi miki magana akan shirmen da ki ka yi kina yi min maganar na shigo ɗaki without permission?."  Islaha ta bi sa da kallon mamaki, ita dai bata ga abin ɓacin rai haka daga wajansa ba, ita ta yi tunanin bazai ji haushi ba, ita ce zata ji haushi, tunda jikinta aka gani ba nasa ba. Meye dan wani ya ganta tana wanka zai ɗaga hankalinsa haka, kamar ya ga matarsa ko wata ƴar uwarsa?.  Ita kunya take ji ta rufe ta, daga ita sai ƙaramin towel a tsaye, ga kanta ko ɗankwali babu. Ta ɗan juya baya da nufin ta ɗauko hijjab, ya finciko hannunta ya dawo da ita ta baya.  Kafin ta ce wani abun ya ce, "dan kin saba yin hakan a wani wajan, shiyasa za ki yi a nan?."  Bata yi niyar tanka masa ba, amma jin abinda ya ce sai ta kawar da duk abinda take ji, ta danne duk wata kunya da firgici ta ce, "tunda ka san na saba meye na zuwa ka same ni kana yi min shouting? Yau wani ya saba ganina ina wanka, ko ka manta har ta ya ni wankan ana yi?." Duk da babu haske sosai a ɗakin, tana iya ganin yadda fuskarsa ta canja kamar ba shi ba. Ita wallahi mamaki yake bata, ko ina ruwansa oho. Ta cire hannunsa da ya riƙe hannunta ta ce, "kar ka sake riƙe hannuna na faɗa maka, ka daina ƙoƙarin taɓa jikina. Ina ruwanka dan ya ganni ina wanka? Kai ya gani kana wankan, ko matarka ya gani, ko ƙanwarka ya gani da zaka damu har haka?." "Na ga dai Islaha ya gani tana wanka ba kai ba ko, to meye na damuwa har haka?. Ai ba yau na saba ba, ka manta na saba zama dashi, ko ka manta kafin shi akwai maza da yawa da suka ganni a irin yanayin da ya ganni?." "Meye naka, abu ne da na saba wannan ba komai bane a wajena. In na ga dama zan kwance towel ɗin jikina in fita kan titi, rayuwata ce ba taka ba, jikina n...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters28
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play