FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciyar Hausa | Mai zana duniya da labarai masu taɓa zuciya da barin tunani mai zurfi.
Sample · 1. Waye shi?
Alhaji Muhammad sadiq wani attajiri ne da yake cikin garin Abuja dake unguwar Maitama. Yana ɗaya daga cikin hamshaƙan masu kuɗin Nigeria. Dalilin hakan yasa ya zama sanennen mutum a duk faɗin ƙasar. Ya mallaki gidajen mai bila adadin sannan yanada companies dayawa da ake sarrafa kayan abinci masu inganci, ga kuma tafka tafkan gidan gonakai. ʼYar sa ɗaya tak a duniya. Sanadiyyar haihuwarta Allah yayi wa matarsa Maryama rasuwa shekaru goma sha tara da suka wuce. Bayan rasuwarta ne aka mayar da sunan ta zuwa ga yar data haifa. Alhaji Muhammad sadiq ya sake aure bayan shekaru huɗu. Ya auri Hajiya zainab wadda ake ƙira da Umma. Hajiya Zainab bata taɓa haihuwa ba domin ita ba mace mai haihuwa bace. Dalilin mutuwar auren ta na farko kenan kafin Alhaji Muhammad sadiq ya aure ta. Hajiya Zainab ta ɗauki son duniya ta ɗaura wa Maryama tamkar 'yar cikin ta. Tana matuƙar kula da ita s...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.