GADAR TSAUTSAYIFree

ArewaPen original

ActionFreeCompleted

GADAR TSAUTSAYI

  • 1views
  • 40chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

Hausa novel writer

More from @nusybee143

Sample · GADAR TSAUTSAYI 1

💫❣️*GADAR TSAUTSAYI*💫❣️✍️Alƙalamin Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)Marubuciyar;Matar khalees Barrister Hibba Siraɗin uƙuba Kaddararmu ce ta zo a haka Masarautar Kaizur And nowGADAR TSAUTSAYI SANARWA!Littafin GADAR TSAUTSAYI ƙirƙirarren labari ne,ga duk wanda ya hali ko suna ko gari ya zo daidai da shi,to a rashin sani ne🙏GARGAƊI!Littafin GADAR TSAUTSAYI mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a chanja ko a juya min littafi na ta kowacce fuska baHaka nan ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izini na *BOOK ONE*Page 1*DSS HEADQUARTERS,KANO STATE, NIGERIA*Ƙaton office ya yi shiru tamkar babu wani mahaluki a ciki,baka jin ƙarar komai sai na kaɗawar AC ɗin da sanyinta ya wadaci katafaren office ɗin,tamkar dai babu wani mahaluki a cikin office ɗin Sai dai mutane ne sun kai goma sha biyu a zaune a jere akan kujerunsu, waɗanda suka kasance manya manyan masu riƙe da muƙami kala-kala a fannin nasu na ƴan sanda,ɗaya daga cikinsu, wanda ya kasance shine shugabansu,wato S.D Ibrahim Haruna yalwa yana tsaye yana fuskantar su fuskarshi babu alamun walwala,da alamu shine cheif officer ɗinsu,kuma yana yin wani bayani ne suna saurara Sake jan numfashi ya yi, cikin ɓacin rai ya cigaba da magana"Wannan abun kunya ne a gare mu,a ce wai wannan ƴarinyar da da yawanmu mun haife ta amma ta gagare mu a cikin garin nan Gaba daya ta lalata mana gari,ta lalata mana matasa, lafiya ƙalau zata yi order na kayan maye ta shigo da shi Nigeria,ta rabawa distributors dinta ta koma inda ta fito,amma an rasa wanda zai iya kama ta a cikinmu?Me hakan yake nunawa kenan?ba mu da amfani ko yarinyar bayanmu ta fi ƙarfinmu?Na gaji da ji da ganin gazawarmu hukumarmu akan yarinyar nan, tabbas wannan gazawa da abin kunya ya yi mana yawa,kuma wannan abin kaico ne"Ɗaya daga cikinsu ne ya ɗaga hannu cikin girmamawa, chief officer ya ba shi izinin magana, cikin sanyin murya ya ce"sir!Yarinyar nan fa ina zargin akwai waɗanda suka tsaya mata a sama, shi yasa take cin karenta babu babbaka,har ta kasa kamuwa kuma ta cigaba da samun confidence na aikata abubuwan da take yi "Cikin ɓacin rai state director ya dube shi,kai tsaye ya ce"babu wanda ya tsaya mata,ita ta tsaya da ƙafarta,kuma ta hana mu tsayawa,kuma ba zan fasa faɗin cewa mun aikata abin kunya ba,da muka gagara samun nasara akan yarinya ƙarama irinta "Shiru office ɗin ya ɗauka kowa yana saƙa da warwara,don dai an san maganar state director gaskiya ce,shekaru biyu kenan ana chasing wannan matashiyar yarinyar amma an kasa yin komai akanta, dole su san abin yi ko hukumarsu ta zama abin dariya a wajen al'umma A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya buɗe,ya ɗaga kanshi a hankali ya kalli hoton yarinyar da yake kafe a ƙaton majigin da yake office ɗin,fara ce tas,...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters40
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play