FreeArewaPen original
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
- 1views
- 104chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH)@Gureenjo on Arewapen@Gureenjih6763 on *** ADABI WRITERS ASSOCIATION#TRIO OF TALES(Three minds, Three stories, one journey.)TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.BOOK1*SHAFI NA ƊAYA**SHIMFIƊA*Farar mota ce mai matsaikacin kuɗi ƙirar lexus ke tafiya cikin natsuwa babu gudu bare rough driving, daga gani matuƙin ba yaro bane ko kuma ya iya kasancewa yaron amma mai tarin sani akan harkar tuki da kuma dokokinta, idan ka tsananta nazari kuwa zaka fahimci ana bin motar a hankali ne saboda wanda ake tuƙawan ba abin wasa ba ne ko na ganganci.Daga cikin motan mutum huɗu ne, ɓangaren mai zaman banza akwai wani matashin saurayi da ya fi yanayi da ɗalibin neman ilimi, sanye da jumpa mai sauƙin kuɗi har da hula rungume da wasu tarukuce na briefcase, Laptop da sauran gadget.A baya ɓangaren hagu nan ma wani matashin ne amma da alama zai iya girmewa wanda ke zaune daga gaban a shekaru, fari ne sanye da baƙar Thobe (jallabiya), ya ɗora hular taɓani-ka-ji-hadisi fara a kanshi mai matsaikacin gashi, fuskarshi cike da saje haka kuma hankalinshi gabaɗaya na ga gefenshi da magana mai sanyin amo ke tashi cike da wani irin natsuwa da waenda ke cikin motan ba don sun natsu kuma sun kasa kunne ba babu abin da zai sa su ji me yake cewa.Mai maganan dake zaune daga ɓangaren dama ya ɗan muskuta, tare da ambaton Allah ya yi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya cigaba da magana a hankali.Duk inda kake neman natsuwa da kamala a kallo ɗaya da zaka yi wa wannan bawan Allah ka same su ka gama, daga yadda yake zaune za ka fahimci dogo ne, yana da matsakaicin jiki amma da alama ƙarfaffe ne, yana da haske fari ne fat, fuskarsa da cikakken gemu wanda da alama ba'a taɓa shi iyakaci gyara, idanunshi sakaye da wasu fararen madubi amma hakan bai hana bayyana natsuwa da zurfinsu ba.Sanye yake da Grey Thobe ya ɗora baƙar shara sharan alkyabba irin ta Larabawa wanda ake kira (jubba) a kai, kanshi akwai Ghutra(wannan gyalen da aka san Larabawa da ɗora wa a kai mai kalar ja da fari da ya zauna mishi sossai a saman ta kuma akwai Agal (wannan baƙin abu mai yanayi da gammo wanda ke hana Ghutra faɗuwa idan ana iska) agogo mai sauƙi amma tsadar a bayyane take ɗaure a tsintsiyar hannunshi, hannunshi ɗaya jikin motar ɗayan na daga kan kafafunshi yana cigaba da yi wa na gefen magana."Ammar ina fatan ka fahimta?""Eh Shehi, In shaa Allahu za'a yi komai yadda ka ce"Kai ya gyaɗa kan ya mayar da ida...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.