GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

  • 1views
  • 52chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · *🪻GAƊAR GIWA...🪻*

Daga Alƙalamin... Ayeesha Abdulkareem ( INDO) بسم الله الر حمن الر حيمRana tsaka  kimanin ƙarfe 01:00 na rana,  a wannan lokacin ba abin da  Hamdan ke yi face Kaikomo a Office ɗinsa, wanda ya ƙawatu da tsadaddun  kayan alatu na more rayuwa.  A kowane harbawar Second ji yake tamkar lokacin yana ƙara nesanta shi da farincikinsa ne, wani irin zafi ke ƙara karyo masa tun daga ƙasan zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa, duk sanyin AC da ya cika ɗakin fal! ba ya ratsa fatarsa  bare har jikinsa ya amsa.Dakatawa yayi da zagayen ya nemi guri ya zauna kan luntsumemiyar kujerarsa wadda ke fuskantar table .Tafukan hannunsa ya ɗora akan fuskarsa tare da furzar da wani zazzafan huci,  wayarsa ya janyo gami da zuba mata ido nan take dukkan  sassan Zuciyarsa masu faɗa a ji suka shiga muhawara.Sai da ƙyar ya iya tsaida  shawara ɗaya, dan haka ya shiga laluben wata number ya  tura kira.A ɗayan ɓangaren Jiki a sanyaye ta kara wayar a kunnenta gami da yin sallama sai kuma tayi shiru don jin abinda zai biyo baya...  "MAA-MA!" Taji an furta sunan da Ƴaƴan cikinta suka saba kiranta da shi, nan take zuciyarta ta yi wata ƙwaƙƙwarar bugawa, "Na'am! waye ? da wa nake magana?"  ta fada cikin kaɗuwa, "HAMDAN AHMAD (MAI MATASA)!"  Ya bata amsa cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa,  cikin sauri  ta maimaita sunan kafin ta ɗora da cewa "Lafiya Kuwa?" "Lafiya lau, HIBBA nake nema"  "Allah Yasa ba laifi ta yi ba!" jim ya ɗan yi yana sauraren yadda zuciyarsa ke bada wani ƙwaƙƙwaran duka, ga wani nauyi da take kara yi masa, a takaice ya ce "Neman ta nake, ina so in gaishe ta!" sai da ta samu gurin zama sannan ta sauke ajiyar zuciya, cikin fara,a wadda ta fi kama da ta yaƙe ta ce "Yanzu  ba ta nan, idan ta dawo zan ba ta wayar sai ku gaisa!"   "Maa-Mah!  so nake in ganta, don Allah ina zan same ta?"   kasa cewa komai ta yi har sai da ya sake kiran ta da "Maa-ma" sannan ta numfasa ta ce "Hamdan! ka yi haƙuri don Allah, Hibba tana farinciki a halin da take  yanzu, kar ka zamo Barazana ga wannan farin cikin namu!"   Runtse idanunsa yayi da sauri hakan ya ba wa zazzafar ƙwallar da ta cika idanunsa damar sauka,  sai da ƴan sakanni suka shuɗe kafin ya iya cewa "Hibba Yar Uwata ce!, ba zan taɓa yin abin da zai cutar da ita ba, sai dai kuma ba a tara sani ga Allah kuma Ƙaddarar da Ta Faru ita ce ake sanin Matsayarta, dukkanmu babu wanda yasan Yaya Ƙaddararsa ta Gobe take!"    Shiru ya yi, a nata gefen ma ta kasa magana sai maimaita zantukansa take a zuciyarta.   Dan janye wayar ya yi daga kan kunnensa  ya ja wani bahagon numfashi ya sauke kafin ya kara wayar ya ce "Ina ne wajen Aikinta?"    "Hamdan! Don Allah kar........

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters52
premium20
01

*🪻GAƊAR GIWA...🪻*

Free sample
Updated 3 months agoAvailable now
02

*🪻GAƊAR GIWA...🪻*

Free sample
Updated 4 months agoAvailable now
32

Gadar giwa

Premium
Updated a month agoAvailable now
33

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
34

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
35

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
36

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
37

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
38

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
39

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
40

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
41

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
42

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
43

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
44

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
46

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
47

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
48

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
49

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
50

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
51

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
52

Gadar giwa

Premium
Updated 3 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play