MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)

  • 1views
  • 9chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

✍️ Rukayya Yusuf Ibrahim Founder | A.Y.M Creatives 📚 Storytelling & Creative Writing 🎬 AI Movies & Visual Storytelling 🎨 Graphics & Branding 🎙 Voice Over & Advertising Creating Ideas That Inspire. ✨

More from @aymcreatives

Sample · MARTANI Episode 0ne

MARTANIA Story of RetributionRukayya Yusuf Ibrahim (A. Y. M Creatives)Arewapen!@https://www.arewapen.com/u/aymcreativesGMJ/26/49GODIYABismillahir Rahmanir RahimAlhamdulillahi Rabbil 'Alamin.Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (Subhanahu wa Ta'ala), Mai kowa da komai, wanda Ya ba ni lafiya, lokaci da ikon fara wannan aiki. Ina roƙonSa da Ya ba ni damar kammala shi cikin alheri, Ya sanya abin da ke cikinsa ya zama haske, nasiha da darasi ga al'umma. Allah Ya sa duk wanda ya karanta wannan littafi ya amfana da saƙon da ke cikinsa. Amin Ya Rabbal 'Alamin.Ina miƙa godiya ga dukkan iyaye, malamai, 'yan uwa, abokai da masu ƙarfafa mini guiwa da addu'o'insu. Allah Ya saka musu da alheri.SADAUKARWANa sadaukar da wannan littafin ga duk wanda ya taɓa yin kuskure ya yi nadama, ga duk wanda aka zalunta yake jiran adalci, da kuma masu imani da ƙaddarar Allah, masu yafiya, da masu haƙuri a lokacin jarabawa."Allah Ya sanya wannan aiki ya zama sanadin ƙara mana kusanci da gaskiya da adalci. Amin.SHIMFIƊARayuwa cike take da ƙaddara, Ruɗani da sakamakon laifikanmu. Wasu kurakurai kan zama ƙanana a idanun masu aikata su, amma zunubinsu kan shafi rayuwar mutane da dama.MARTANI labari ne da ya ginu a kan soyayya, zalunci, yaudara, nadama, tarbiyya da sakamakon abin da mutum ya aikata. Yana ɗauke da darussa da za su tunatar da mai karatu muhimmancin tarbiyyar yara, adalci, gaskiya, yafiya da kiyaye haƙƙin mutane.Ina fatan wannan littafi zai nishaɗantar da ku tare da ilmantarwa, ya kuma zama abin tunani ga duk mai karantawa.GARGAƊIMARTANI ƙirƙirarren labari ne. An rubuta shi ne domin nishaɗantarwa tare da isar da saƙo da darasi ga al'umma. Duk wani kamanceceniya da sunaye, wurare ko abubuwan da suka faru da rayuwar wani ko wata, kamanceceniya ce kawai ba da gangan ba.Haƙƙin mallakar wannan littafi na marubuciya ne.Ba a yarda a kwafa, a sake wallafawa ko a juya shi zuwa kowace siga ta (audio, fim, ko wani tsari), ko a rarraba shi ta kowace hanya ba tare da izinin marubuciya ba. Yin hakan ya saɓa wa dokokin haƙƙin mallaka kuma za a ɗauki matakin da ya dace. بسم اله راحمن ارحىم"A'isha...A'isha.. A'isha.." Umma ta kira sunan A'isha da karfi cikin daga murya.Fitowa tayi cikin natsuwa tana cewa "na'am Ummana gani nan zuwa ".Jugum wacca aka kira da Umma tayi , tana jiran zuwan A'isha.A'isha ta nufi gurin da take tana duban Umman ta ce " gani Umma me ya faru ne ?" . Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta dan yi shiru kamar me nazari sai kuma ta ce" kawunki ya zo ɗazu bayan kin fita makaranta".Dafe ƙirji tayi idonta sun ƙwalalo waje alamar firgici tana duban Umman cikin rawar baki ta ce" ba dai maganar fitar da mijin yayi miki ba?".Sauke zazzafan numfashi tayi hannunta kan sandar da take gefenta ta fara cewa " hakuri zakiyi A'isha domin wannan karon ba ma zancan ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters9
premium4
05

Episode 05

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
06

Episode 6

Premium
Updated 3 months agoAvailable now
07

Episode 07

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
08

Martani Episode 8

Premium
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play