TAURARI BIYUFree

ArewaPen original

TAURARI BIYU

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writer

More from @queenmeemi

Sample · Taurari biyu

TAURARI BIYU (Two Stars)Meemi Basheer*Sabon labari, daga meemi bashir Taurari Biyu (Two Stars) zai ringa zuwa muku a shafina na* *Arewapen app. Username:* #queenmeemi#Haka kuma a **** #queen-meemi da kuma *** group da channel.*Bisimillahir-rahmaninr raheem.*Chapter 1Babbar mota ce ta fito daga tashar motar  wani karamin gari Mai suna Quezzam da ke  ɗaya daga cikin garuruwan ƙasar Aljeriya. Motar cike take da mutane, mabambantan yaruka, Tuareg , Zabarmawa, Fulani, Kanuri, Buzaye,hausawa da sauran masu shigowa ƙasar don ci-rani. Da dama Akwai Tuareg  da ke fita fatauci daga Quezzam zuwa wani ƙauye da ke kan iyakar Nijar da Aljeriya mai suna Assamaka, inda yanzu ma suka nufa.Mutanen cikin motar na ta korafi kan yadda direban ke yawan tsayawa akai-akai, abin da ke janyo musu ɓata lokaci a hanya Kenan. Tsaki na yi tare da kallon agogon hannuna na ga har ƙarfe goma sha biyu na rana ta yi. Na lumshe ido domin ina son yin barci, wanda ya zama min al’ada idan zan yi tafiya mai nisa.Amma surutun Ruman, wadda ke zaune kusa da ni, ya hana ni barcin. Na muskuta tare da juyar da kai, na ɗan bugi bayanta don ta yi shiru. Ita ma ta san ba zan iya barci cikin wannan hayaniyar ba, balle ga matsin da muke ciki da yadda motar ke rangaji a tsakiyar Sahara.Na ji an daki ƙafata da ƙarfi, har sai da na ji zafi. Na buɗe ido da sauri, na sauke su kan mutumin da ya buge ni. Idanunsa suna cikin rawani, amma sun ja sun yi jajir.Na Harare shi tare da dauke kaina, Sai na samu kaina da sake kallonsa, take na Ji wani irin rashin yarda da shi ya mamaye zuciyata. Na gyara zamana, na ci gaba da kallonsa kai tsaye. Shi ma ya kafe ni da ido.Sai na kau da kai cikin rashin jin daɗi. Wani yanayi ya mamaye ni irin wanda nake ji idan ban yarda da mutum ba. Da alama ya fahimci wani abu, sai ya gyara rawanin kansa ya ɗaga shi kaɗan, sannan ya dubi wani kusa da shi ya jinjina masa kai.Jikina ya ɗan shiga  rawa, na shiga murza hannuwana a cikin hijab. Ban san dalili ba, amma na kasa daina kallonsu.Bayan doguwar tafiya, direba ya sanar da mu cewa za a tsaya domin sallah. Ya tsaya a wani ƙaramin gida da yake shi kaɗai a wajen, muka fito gaba ɗaya.Ni da Ruman muka yi alwala, muka yi sallah. Wasu kuma suka fara cin abinci.Na ja gefe na tsaya ina cin gurasa da lemon roba da na taho da shi. Sai na Ji tashin magana sama sama cikin yaren tuareg , juyar da kai na yi ba tare da damuwa ba! maganganun su suka ringa ratsa kunnuwana, na samu kaina da son leƙawaNa matsa kusa sosai ina sauraro.“Ina ganin mu kawar da shi idan mun isa Asamaka. Bayan mun gama aikin da aka aiko mu, ba zai wuce awa biyar ba ya mutu.”Kaina ya ɗaure. Ban fahimci abin da suke nufi ba, amma na tabbatar akwai wani abu mai haɗari. Na yanke shawarar sa musu ido.“Kowa ya shiga mota, za mu ci gaba da taf...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play