FreeArewaPen original
Hawayenmu
- 1views
- 70chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
*HAWAYENMU!* BYSADIYA ABDULRAZAK MARUBUCIYAR Kuyi mana adalci Dukan taiki Rigar ƙaya Zuciyar maceIya ruwaWani aurenSandar dukan uwargida Aure A Yau da sauransu*** Page 1 Jiki a matuƙar sake take taka ƙafa a cikin unguwar tasu, tana shiga zauren gidansu hawayen da take riƙewa suka rinjaye ta, ta sake su babu shiri, tsakar gidan cike yake da mutane, matan gidan kowa yana sana'arsa da kuma masu siyan abin da ake siyarwar, haka ta keta su ta wuce riƙe da takardar gwajin nata tana hawaye, hakan ya saka matan babanta Dije da Uzaiba suka kalli juna cike da zargi. Tana shiga ɗaki ta ɓarke da kuka tana jifa da takardar.Mairo ta taso da sauri tana faɗin "Ke Farida! Lafiya? Me ya faru a wajen gwajin?"Ta ƙara ɓarkewa da sabon kuka "Inna ni dai daga wannan na haƙura da auren nan, shi ma jininsa AS ne, babu damar mu yi aure, ƙaddarata ce rashin aure na haƙura kawai".Mairo ta ce "Kul! Kar na sake jin haka daga bakinki, ƙaddara ce, amma ba za a dawwama a haka ba, in sha Allah komai zai zama labari kin ji ko?""Allah Ya sa". Ta kwanta a gadon ƙarfe tana haɗe jikinta, sabon kuka yana ciyo ta, kusan za ta ce duk samarin da ta yi ba ta yi wa wani son da take yi wa Khamis ba, ba ta yi zaton haka za ta faru ba sam, wannan shi ne karo na uku da aka fasa aurenta bayan ta gama sakankancewa ta samu miji, kuma ta saka a ranta daga wannan ya isa haka, ta haƙura da saka wani namiji a ranta, tun da dai ta lura a ƙaddararta babu zama matar aure, ƙannenta duka suna ɗakin mazajensu kowacce da yaranta, ita kuma har yanzu abu ya ƙi tabbata.Wajen minti talatin tana kwance kafin Inna ta ce "Wannan kwanciyar ba za ta kai miki ba ai Farida, tashi za ki yi ki tafi gidan aikinki"."Zan tashi"."To jiranki za ta yi gida ba gyara? Motsa ki je, fasa auren kamar yau ne karon farko? Idan da sabo ai ya ci a ce kin saba ma, na ga wannan dududu ma yaushe kuka haɗu?"Ta tashi ta je ta wanke fuskarta ta saka hijjabi ta tafi, tafiya kaɗan ta kai ta wani gida me babban gate, ta buga tana faɗin Farida ce, aka buɗe mata ta shiga. Hajiya Amina tana zaune a falo tana latsa waya, amma kuma hawaye take yi, don chart take da ƙawarta tana faɗa mata damuwarta, Farida ta shiga da sallama, ta ɗauke hawayen da sauri sannan ta amsa tana aro murmushi ta ɗora a fuskarta ta ce "Farida yau ya aka yi kika yi latti?"Hawaye ya goce mata ta ce ita ma ta share ta ce "Na je asibiti ne". "Subhanallah! Asibiti kuma? Ba ki da lafiya ne?""Lafiyata ƙalau gwaji muka je...""Kar dai shi ma AS ne?" Ta tambaye ta, don suna fira da Farida ta san duk labarinta.Wani hawayen ya kawo a idon Farida ta ce "E Anti, shi ma haka".Ta sauke numfashi "Allah mai iko, wato dai duk yawan masu genotype AA akwai masu AS ma da yawa, kamar yadda duk yawan matan ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.