FreeArewaPen original
GABA TAZO BAYA
- 1views
- 27chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
GABA TAZO BAYAUmmulkhair S Panisau (Khairatup)001"Don Allah ki sake bani dama na zamo mijinki a karo na biyu Nihila Wallahi na gane kurena,zan gyara abinda na ɓata."Wani irin kallo na jefa masa irin kallon anya kuwa kana cikin hayyacin ka kuwa. Ban kai ga cewa komai ba ya sake tare mini numfashi."Ki tuna tun bamu gama sanin rayuwa ba muke tare kina ganin za ki iya rayuwa ba tare da ni ba?"A wannan gaɓar na saki wani irin murmushin taƙaici na juya kamar zan tafi sai na kuma juyowa na kalle shi ido cikin ido."Wallahi Abdullahi baka da kunya." Yadda ya zaro idanunsa waje ne ya saka na gane cewa mamakin abinda na faɗa yake yi. Don na ba shi tabbaci na sake ce masa "Nace baka da kunya Abdullahi,kai yanzu ka yi wa kan ka adalci ba ma ni ba? Wai na tuna zaman mu to me kake so na tuna a zaman namu? Ne zan tsinta banda kayan takaici da baƙinciki ? Kar ka sake zuwa ƙofar gidanmu ka ce wa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.