FreeArewaPen original
SANADIN HIJIRA
- 1views
- 31chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writer ✍️ | Storyteller 📖 Creating stories that touch hearts. ❤️
Sample · Chapter 01
SANADIN HIJIRA By 💞UMMU FADEELA💞TYPING📲*CHAPTER 01.* (ABUJA NIGERIA)...........A gaggauce ta ke tura abincin bakinta tamkar zai gudu ya barta,duk ta 'bata tsakar kitchen din da rice kai kace kaji ne suke dambe a wajen.Tsaye ta ke gaban tukunyar da bai juma ba aka sauke duba da yadda hadadden jollof d'in ke tururi, amma haka take jefa hannu ciki tana dumbusan abincin gami da cusawa a bakinta yayin da rabi ke shiga bakin saura ku ma yake bin jikinta kana ya gangara kasa ya watse.Duk yawan abincin haka ta caccakala shi ta watsar gami da ture tukunyar gefe,ledan biredi dake gefe ta janyo ta yageshi da karfin tsiya ta yanko wanda yafi karfin bakinta har ta nufi bakin dashi sai kuma ta tsaya tana kare mishi kallo kamar mai son karantar yadda aka sarrafa shi,goga shi ta farayi saman kanta da babu dankwali tana bubbugawa da karfi karfi sannan ta cire ta yayyanka shi into pieces da hannunta ta watsar a tsakar kitchen din.Da hanzari ta koma bakin sink ta kunna ruwa ta kafa kanta akai ta fara daddaka like her life depend on it,ruwa tasha fiye da kima sannan ta nufi hanyar fita kamar ba ita ta yi barnar ba.Kofar kitchen din ta bude a hankali,kanta da babu dankwali ta leka ta tsakanin kofa da jikin ginin,kamar wacce take fahimtar abun da ke faruwa take kare musu kallo.Hamshakiyar macece wacce ta amsa sunan hajiya ta ko wanne bangare baƙace amma jikinta yana sheki da walwali irin na hutu da jin dadi da suka samu matsugunni a gareta,shigar jikinta ta alfarmace kai kace first lady ce a wajen taron mata HAJIYA FANTA,gefen hagunta wata matar ce itama da za'a kirata da hadaddiyar mace HAJIYA TITI, suna zaune bisa kujera mai zaman mutum uku suna tattaunawa kasa kasa....Wulkita idanunta ta yi zuwa daya gefen na cikin kasaitaccen palon da ya amsa sunan palo,still akan kujera mai zaman mutum uku wata matashiya ce da akalla zata kai shekaru talatin a duniya,jibgegiya ce sosai irin masu jiki mai gaɓa gaɓa dinnan,tana sanye da vest wadda ya bayyana damatsenta tamkar yar wrestling kanta dauke da hula sai single zani da ta daura hannunta rike da waya tana aikin daddanawa,SAUDAT,kusa da ita wata ce da zata iya kaiwa sa'anta itama katuwa ce sosai kana bata cika tsawo ba,fuskarta farine sol amma pimples yayiwa hasken tarnaki dan ya cika fuskar taf babu masaka tsinke,wanda hakan ke tabbatar da hasken ba nata bane janyoshi ta yi ta hanyar dole duba da hannunta da kafafunta da suka kasance baƙaƙe,sanye take da doguwar riga mai yankakken hannu na shan iska kwance bisa kujerar tayi filo da cinyar Saudat itama tana ta faman danna waya kamar rayuwarsu ya dogara a kaine kacokam.BADARIYYA.Takawa ta farayi zuwa cikin palon,bata da wani jiki salau salau take kamar ka hure...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.