FreeArewaPen original
Soyayya ko Zalunci
- 1views
- 37chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Babi na days
Bismillahir rahmanir rahim… “Kar ki zo daga baya kina cewa da-na-sani. Shawara muke baki. Duk namijin da zai zo yana kushe matar gidansa a gaban budurwarsa, to wallahi wannan ba mijin aure ba ne.” Muryar Siyama ce ta fito daga cikin wayar cikin nuna damuwa da takaici. Fatima na zaune a gefen gadonta, ta jingina bayanta da bango yayin da take sauraron conference call ɗin da yayyenta biyu, Siyama da Qawwama, suka kira ta. “Fatima, mai son ki shi ne yake gaya miki gaskiya,” Siyama ta ci gaba da magana cikin natsuwa. “Kin yi babban kuskure da kika yarda aka sa ranar aurenki da wannan mutumin.” Fatima ta ja numfashi a hankali. Tun kafin Siyama ta gama magana, ranta ya riga ya ɓaci matuƙa. A ganinta, babu wanda yake fahimtar Muktar kamar ita. Duk lokacin da yayyenta suka fara magana a kansa, sai ta ji kamar suna zaluntarsa ne ba tare da sun san hakikanin halayensa ba. “In shaa Allahu,...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.