KARFE DÜKKA KARFE NEFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

KARFE DÜKKA KARFE NE

  • 1views
  • 19chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

"Life is short, break the rules, forgive quickly, kiss slowly, love truly, laugh uncontrollably, and never regret anything that made you smile."

More from @maidambu41

Sample · BABI NA DAYA

KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!  {Zanen ƙaddarar Falilah} Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai... Started 1/17/2023 Realize 29/6/2026    Barka da Sallah yan uwa musulmai. _Wannan karon nace bari na kara tsakuro mana da wata rayuwar da yaƙe cikin yankin kasar hausa, ban sani ba ko yayi daidai da zab'in ku, gare ni ya min daidai da zamanin da muke ciki, Allah ka bamu ikon rubuta dai-dai Amin Ya Allah_ (True life even) BABI NA ƊAYA...            Murmushi na sake lokacin da naji kid'an da yake tashi a wayar tafi da gidan ka, wadda ya kasance mallakata ce. Juya fararren idanuna nayi akan shi, kafin na kai hannuna na dauki wayar ina me kallon sunan wadda yake kan wayar. "Hmm!" Shi ne sautin murmushi na da ya fito daga bakina, sannan na dauki wayar a hankali gudun kar ta tsinke.  "Amincin Allah shi tabbata a gare ka, Mijin Mariyah Angon Falilah." Na fada ina hadiye yawun bakina, murmushi yayi sannan ya ce min. "Amin tare da ke Falilahta, ina kewar ki ainun gashi aiki ya min yawa balle na katse."  "Haba! Ina, yi aikin ka a hankali, kai da zaka dawo gidan ina jiranka, baki daya gidan ya min fad'i ne ba kowa." Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya, kafin ya ce min. "Lilly! Ina sonki yadda baki ba zai iya furtawa ba. Lilly ina miki mahaukaciyar son da zan iya bada rayuwata domin ki, lilly ki yarda ni Ahmad Lamido na so ki har fitar numfashina, ki had'a min kayana kala biyu gani nan zuwa" "yarrrrrrr" naji tsigar jikina ya mike, a hankali na ce mishi. "Abban Basmah akwai matsala ko?"  "No hada min kaya gani nan zuwa, zan tafi Yola ne yau in sha Allah." "Tow" na iya furta mishi ina sauke wayar a kunnena, sai gyad'a kai nake kamar kadangariya, ji nayi baki daya kamar an daure ni, leka waje nayi na hango haɗari bakikkirin, da sauri na fita ina tattara wankin da nayi na unders din mu, na kai dakina sannan na kuma fitowa zan kwashe shanyar daddawa da busashen kin da nayi, aka fara ruwa. Da gudu-gudu na fara tattara kayan ina shiga da shi part dina, haka kawai na tsaya ina kallon part dina, yau wata na goma sha biyar a gidan nan, wanda zance a cikin watanni nan na mori wasu shudadden kwanaki, na mori wasu abubuwan da na rasa a baya, kai anya zan kuma farin cikin da na rasa a baya? Dafe kirjina nayi ina jin haki da fitar numfashi, hawaye ya zubo min. Ina ma mu dawwama haka ni da Ahmad Lamido, ina ma ni daya ya fara mallaka a rayuwar shi. Nasan Ahmad adali ne, mutum ne me son sauko hakkin iyalin shi, ta ko ina Ahmad ya sauke nauyin shi, nima ta bangarena nayi iya kokarina wurin sauke nauyin shi da na abokiyar zamana wacce haka bai dame ta ba, bai d'ikata da kasa ba, wacce haka bai wani  burge ta ba. saukar ruwan da ya kara jika min kayan jikina yasa ni jan kafana na nufi wurin kayan na kwashe, sannan na...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters19
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play