FreeArewaPen original
RIGAR ARO
- 1views
- 109chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwa Manazarciya Marubuciya Ƴar kasuwa Chocolate addict 🍫 Bookworm📗 Introvert 😚
Sample · 1
Sanyin yammacin rana ya ratsa ta cikin gidan, gida ne matsakaici wanda bangon sa ya fara cin kansa saboda tsufa, duk da haka a gyare yake, irin gidan nan ne na talakawa masu rufin asiri average middle-class struggling home. A gefe guda na tsakar gidan, sautin kukan kaji ne ke tashi daga cikin kejin da aka gina da raga, inda kajin ke kai da kawowa suna jiran abinci. A kan wata tsohuwar kujera mai dauke da tsumman matasai, Jaddi take zaune kishingide. Idanunta a lumshe suke saboda raɗaɗin jikin da take ji, jikinta ya nuna alamun sugar ɗinta ya tashi, numfashinta yana fita da sauri-sauri. Daga cikin ɗaki, Nurayyah ta fito, yarinya ce mai kwarjini duk da shekarunta sha shidda ne kacal. Sanye take da doguwar rigar atampa wadda ta zauna mata ɗas a jiki, ta yafa babban hijab ɗinta, ko a yanayin talauci, Nurayyah akwai nutsuwa. "Jaddi, mu tafi lokaci yana tafiya," Nurayyah ta faɗa tana kamo hannun kakar tata cikin kulawa. Sannu a hankali suka fito har babban titi, inda Nurayyah ta tsaida Adaidaita Sahu. "Malam, Barau Dikko Specialist Hospital zaka kai mu," ta faɗa da wata irin nutsuwa. Sun yi ciniki, sannan suka shiga, suka nufi asibiti, Motar adaidaita sahun ta tsaya daidai kofar shiga sashen gaggawa da marasa lafiya na waje, wato GOPD (General Out-Patient Department) na asibitin Barau Dikko. Hayaniyar mutane, kukan jarirai, da kuma warin magunguna da sinadaran asibiti suka tarye su tun kafin su kai ga shiga ciki. Nurayyah ta biya ɗan adaidaitan, sannan ta kamo hannun Jaddi wadda kusan rabi ne kawai na nauyin jikinta take iya dauka, sauran duk ya tafi saboda radadin ciwon da yake ratsa kashinta. Suna shiga ciki, Nurayyah ta ji gabanta ya fadi. Mutane ne birjik a zaune a kan dogayen kujeru na karfe, wasu ma a kasa suke zaune saboda rashin gurbi. Layin katin asibiti ya zama kamar maciji, kowa yana rike da takardarsa yana kallon agogo. Nurayyah ta jawo Jaddi zuwa wani dan lungu, ta samu wata tsohuwar kujera ta zaunar da ita. "Jaddi, bari na karbo mana kati, dan Allah ki danyi hak'uri kinji," Nurayyah ta fada muryarta na rawa. Jaddi bata iya magana ba, sai kawai ta gyada kai, idanunta sun yi luf-luf, launin fuskarta ya sauya daga launin fata ya koma wani irin kalar toka-toka saboda sugar da jikin da take ji. Nurayyah ta koma layin katin, Bayan ta karbo ta dawo tana jira layi yazo kansu, nan ne ta fara ganin abin da ya fi ciwon jiki radadi wato rashin adalci. Mutane na ta faman kukan yunwa da jinya, wasu tsofaffi ne sun kusa faduwa amma ba wanda ya damu dasu kowa ta kansa yake. Idanunta suka kalli wani bawan Allah da aka shigo da shi a keken marasa lafiya (wheelchair), kafarsa a nade da bandeji wanda jini ya riga ya bata duk jikinsa, aka ce masa ya jira sai an duba wadanda suka riga shi saboda akwai layi sosai a wurin. Tana cikin wannan tu...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.