FreeArewaPen original
AAMINAT (Bazawara)
- 1views
- 3chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Aaminat (Bazawara)
*AAMEENAT* (Bazawara)Littafin Haɗaka.Ayeesha Abdulkareem *AUNTY INDO* Tare daSalma Abdulkareem Free page PAGE 1 BismillahirrahmanirrahimKallon Umaimah Fati ta yi kafin ta ce kai wa Waccan Tsohuwar Bazawarar Abincinta, ta yi maganar tana gyatsine Fuska, Umaima ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta ɗauki ɗan Abincin ta nufi Ɗaki da shi.Aaminat ta na zaune ta zuba Tagumi ta na jiyo su amma ba ta da bakin cewa ƙala.A can gefe Umaima ta ajiye Abincin Sannan ta ce "Ga shi nan in za ki ci"rausayar da kai tayi sannan ta taso zata ɗauka, Umaimah ta bi ta da kallon banza kafin ta ce "A haka dai za a ƙare" hawayen da suka cika mata Ido ne suka samu damar gangarowa fuskarta, Umaima ta watsa mata harara sannan ta fice tana jan tsaki.wani sabon kuka ta fashe dashi tana cewa "ka cuceni bazan taɓa yafe maka ba azzalumi" ganin kukan ba ze amfane ta ba yasa ta tashi ta nufi ɗakin wanka ruwa ta watsa ta fito ta shirya cikin doguwar riga Abaya yaluwa taji duwatsu masu sheƙi da walwali tayi kyau sosai madubi ta kalla wasu hawaye masu zafi suka fara gangarowa da sauri ta kauda kai tana tauna laɓɓanta kafin ta tashi ta nufi ƙofa Mama ce tace " zawar zawar ce ta fito kenan" "haba kekuwa Mama ba dole a fita neman bazawari ba" cewar Fati.dariya Su ka sa Kafin Mama ta ce "Allah ya raka taki gona" Aaminat ta murmusa ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar fita, a ƙofar gida ta coge ta na leƙawa, kasancewar yamma ce ga iska na kaɗawa a hankali a hankali ya sa yanayin ya yi mata daɗi sosai, yaran layin da su ke Ƙwallo ta ke kalla, a zahiri idanunta su na kansu amma a cikin ranta tunanin Yau da Goben Rayuwarta kawai ta ke yi, "Wace irin Rayuwa ce Ƴan Adam su ka ɗorawa kansu??, ba sa tunanin ita Ƙaddara ba kai kake tsarawa kanka ita ba??" tunanin da ya fi yi mata yawo kenan, ta na cikin tunanin ta ji saukar Ƙwallon a Fuskarta, ta yi baya cikin sauri gami da dafe fuskar tata, hawayen azaba ne su ka fara tseren zubowa kan kumatunta, yaran su ka yo yuuu akanta wasu suna "Don Allah ki yi haƙuri" wasu kuma su na cewa "Wallahi Walid ne ya jefo miki ita" Goge hawayen ta yi ta ɗago fuskarta ta na kallonsu, murmushi wanda ke ƙara nuna zallar haƙurinta ta yi kafin ta ce "Na haƙura" Sauran su ka Ɗauki Ball ɗin su ka koma wasa. Abdulkareem ne ya tsaya Ya na Kallonta cike da tausayawa, "Yaya Aamimat!" ya kira sunanta cikin sigar Tambaya, cikin sauri ta zuba masa idanu, sai a lokacin ma ta san ya na gurin domin kuwa a kowacce daƙiƙa tunani ne tsarin rayuwarta, "Abdulkareem sun ci gaba da wasan ba kai" ta faɗa ta na masa ɗan murmushi wanda ya ke bala'in sumar da Zinariyar Zuciyarsa "YaYa Aameenat ban ji daɗi ba, wallah...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.