BANGON MASARAUTAFree

ArewaPen original

FanfictionFreeOngoing

BANGON MASARAUTA

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

TARIHIN DAULAR KILAShekara Dari Biyu da Talatin da Biyar da Suka Gabata (1790)Daular Kila ta kasance ɗaya daga cikin tsofaffin masarautun da suka yi suna wajen adalci, jarumtaka da kuma kare mutuncin al’umma. An kafa ta ne a cikin wani kwari mai yalwar noma, kiwo da kasuwanci, wanda ya haɗa hanyoyin matafiya daga gabas da yamma. Sunan Kila ya samo asali ne daga wani tsohon jarumi mai suna Kilan Dabo, wanda shi ne ya fara haɗa ƙabilu daban-daban ƙarƙashin tuta guda.Tun kafin kafuwar masarautar, yankin ya kasance cike da ƙananan ƙauyuka masu cin gashin kansu. Sai dai yawan rikice-rikice tsakanin shugabanninsu ya hana zaman lafiya. A lokacin ne Kilan Dabo ya tattara dattawa da mayaƙa, ya sasanta su, sannan aka kafa Daular Kila bisa ginshiƙai uku: adalci, gaskiya da haɗin kai.Kafin kafuwar Daular Kila, yankin ya kasance ƙauyuka ne da dama da suke rayuwa dabam-dabam. A wancan lokaci, yawancin al’ummar yankin suna bin addinin gargajiya, inda suke bautar iskoki, manyan itatuwa, duwatsu da rafuka. Akwai wani babban tafki da ake kira Ruwan gujus, wanda ake ɗauka a matsayin wurin tsafi. Kowace shekara ana kai hadaya a bakin tafkin domin neman ruwan sama, kariya daga annoba da yalwar amfanin gona.Dattawan ƙauyukan sun yi imanin cewa ruhun tafkin ne ke ba su albarka, saboda haka duk wanda ya karya dokokin tsafin, ana ɗaukar cewa zai jawo masifa ga ƙasar baki ɗaya.Shekaru da dama bayan haka, wasu malamai masu yaɗa addinin Musulunci suka iso yankin Kila ta hanyar ayarin ‘yan kasuwa daga ƙasashen sokoto da Borno. Sun fara wa’azi cikin hikima da haƙuri, suna koyar da tauhidi, ibada da kyawawan ɗabi’u.Da farko mutane da dama sun ƙi karɓar saƙon Musulunci saboda tsoron barin al’adunsu. Amma a hankali, sakon ya fara shiga zukata. Dattawa da matasa suka fara musulunta, aka fara gina ƙaramin masallaci na laka, sannan aka fara koyar da Alƙur’ani ga yara da manyaLokacin da Sarki Kilan Dabo ya hau karagar mulki, ya rungumi Musulunci tare da manyan fadawansa. Ya bayyana cewa addinin Musulunci shi ne zai zama ginshiƙin shugabancin Daular Kila. Ya rusa wuraren bautar gumaka da tsafe-tsafe, ya hana yin hadaya ga rafuka da itatuwa, sannan ya umarci a gina Babban Masallacin Juma’a a tsakiyar masarautar.Duk da haka, bai tilasta wa kowa musulunta ba. Ya yi amfani da hikima da adalci, lamarin da ya sa al’umma suka riƙa shiga Musulunci sannu a hankali har addinin ya bazu a faɗin Daular Kila.Bayan tabbatar da zaman lafiya da haɗa ƙauyuka goma sha biyu ƙarƙashin tutar masarauta guda, Sarki Kilan Dabo ya kafa tsarin mulki na farko na Daular Kila. Ya kafa Majalisar Dattawa, rundunar mayaƙan fada, da dokokin da suka haramta zalunci, cin hanci da kwace haƙƙin talakawa.Saboda hikimarsa da adalcinsa, ana kallon Sarki Kilan Dabo a matsayin Uban Daular Kila, kuma har bayan rasuwarsa ana ci gab...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play