HAYAT NAZLIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

HAYAT NAZLI

  • 1views
  • 32chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000167069 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000167061ABUJA NIGERIA*. ~ASOKORO~  Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ce wacce a kallo ɗaya za a tantance irin baiwar da Allah ya yi mata na tarin kyau da tsarin halitta, ta haɗa komai na macen da ta samu cikakken gata kuma shalelen iyayenta. Cikin shigar kayan motsa jiki ta ke guntun riga da wando masu faɗi wanda ya ke nuna alamun kaya ne da a ka tanada dan yin exersice. Ga sumanta da ta ɗaure shi da rebom yana reto a gadon bayan ta saboda aikin juya jikinta da ta ke yi cikin sauri-sauri, duk da ta haɗa gumi ba ta tsaya ba sai da ta ji ta gaji sosai kana ta dakata ta janyo wani ƙaramin farin towel ta shiga goge saman wuyanta da fuskarta Kafin ta ɗauko gorar ruwa ta kafa bakin ta shanye ruwan ciki tas sannan ta yarda gorar ta saki towel ɗin da ke saman kafaɗarta ya yi ƙasa.     Wani juye ta yi tamkar babyn roba tare da sarƙe hannayenta a ƙirjinta tana barin ɗakin games ɗin cikin sassarfa, kai tsaye katafaren ɗakin da ya ke mallakinta ta nufa wanda yaji kayan alatu da more rayuwa a ciki da a ka kashe maƙudan kuɗi duk dan a ƙawata bafin cikinta, ƙamshin sanyayyen turaren wuta da ya gauraya da sanyin AC ya mamaye cikin faffaɗan ɗakin.  Kan royal bed ɗinta ta zube tana mayar da numfashi tare da lumshe idanunta kana ta buɗe su, sai kuma kamar wacce aka tsikara ta sauko daga gadon ta faɗa toilet ta sakar ma kanta ruwa. Manyan idanunta da suke ɗauke da kalan blue ta shiga warewa a hankali ruwa na cigaba da shiga cikin su, gashin kanta kuwa yana kwanciya yala-yala akan kyakkyawar farar fuskarta. Duk inda a ke neman mace me aji da kuma kyau idan a ka zo kan ta an gama. Furzar da ruwan da ke shigar mata baki ta yi tana mai maida gashin kanta da ya rufe rabin fuskar ta baya, a hankali ta soma gudanar da wanka tana mai bin sassan jikinta a sannu, bayan ta gama wankan ta ja bathrobe ta sanya, sannan ta ɗauki towel ta tsane sumar kanta, bayan ta gama ta fito ta nufi wajen madubin ɗakin ta ja stool ta zauna, Sannan ta soma busar da gashin ta da haire dryer. Mayukan gashi masu ƙamshi ta shafa kana ta haɗa ta yi parking na shi a tsakiya yayinda ta bar jelar gashin ke rito a gadon bayan ta.  Hoda da man laɓɓe kawai ta shafa sai kwalli da ta saka a ƙurmin ido wanda ya ƙara fito da kyawun su tare da girman halittar su. Ƙarar ringing ɗin wayarta da ke kan gado ne ya jawo hankalinta wajan, wani ƙayatattan murmushi da ya bayyana dimples ɗinta ta saki yayin da ta ɗaga wayar da faɗin.  "Assalamu' alaikum Daddy, amincin Allah ya tabbata a gareka. Fatan ka tashi lafiya?" Ta ɗayan ɓangaren a ka amsa da:  "Albarka ya tabbata ga ƴata da iyalan ta, fatan Nazli din Abba ta tashi cikin ƙoshin lafiya?" "Al...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters32
premium8
25

25

Premium
Updated 20 days agoAvailable now
26

26

Premium
Updated 20 days agoAvailable now
27

27

Premium
Updated 20 days agoAvailable now
28

28

Premium
Updated 20 days agoAvailable now
29

29

Premium
Updated 20 days agoAvailable now
30

30

Premium
Updated a month agoAvailable now
31

31

Premium
Updated a month agoAvailable now
32

32

Premium
Updated 20 days agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play