YARIMA BAHJATFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

YARIMA BAHJAT

  • 1views
  • 16chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Uwar batoorl ✍️ writer Follow me on Whattpad - @Uwar batoorl *** *** *** Gmail - ***

More from @uwarbatoorl96

Sample · Shafi na ɗaya

        🌏 YARIMA BAHJAT 🌏        NaHarira Salihu Isah    (Uwar Batoorl)𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠    اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW Dukkan godiya sun tabbata ga Allah(SWT), da ya ba ni ikon kawo muku labarin sarauta kamar yadda na alƙawarta muku tun bayan kammala ƳAR KARUWA, amma da yake Allah bai nufa ba har muka yi SHAAMEEƘH da NAUYIN BAKI, sai yanzu Allah ya Ƙaddara, to alhamdulillahi, Allahumma ya ba mu ikon kammalawa lafiya, ya kuma haɗa mu a kan ladan duk abinda ya zo na faɗakarwa, ya yafe mana kura-kurai.GAISUWA DA JINJINANi Uwar Batoorl ina gaisuwar jinjina ga duk masoya masu ƙwarara guiwa da ƙarfafa guiwa a gare ni, a saya littafina a yaba mini, a alkairanta mini a kuma a bi ni da addu'o'i, ina jinjina a gare ku, Allah ya muku ninkin wanda kuke mini daga addu'o'i har abin arziƙi, Allah ya taya ni gode muku, madallah da ku.MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA ***.MADALLA DA KUU, UWAR BATOORL TA KUUU.SHAFI NA ƊAYA.....MADUBI  A wasu lokuta da dama, Buri, Muradi, da Nufi, abubuwa ne mabanbanta da su ke bisa doron hanya ɗaya, domin ana iya ɗaura su a mizani guda, kamar yadda su ke sarƙafe da zare guda ɗaya, wato zaren Ƙaddara. Idan aka ce Ƙaddara ana nufin abinda Allah ya rubuta ya kuma zana zai wanzu a rayuwar bawa tun ma kafun samuwar bawan, abu ne wanda bawa ba ya taɓa kauce masa, haka kuma ba ya taɓa iya guje masa duk tsanani kuwa. Ƙaddara wata kalma ce da ke ɗauke da fuska biyu, tsari biyu, zubi biyu, zane biyu, wato kyakkyawa da kuma kishiyarta.A zahirin gaskiya, muna saƙa burukanmu ne kawai da kuma muradanmu, haka ma muna nufin wasu lamuranmu ne ba tare da mun duba cewa Ƙaddara ba ta ba da zaɓi ba, tabbas Ƙaddara ba ta bai wa bawa zaɓi, duk da a wasu lokutan Ƙaddara ta kan zo kafaɗa da kafaɗa ne da muradan mu, amma a wasu lokutan shatale ƙafafuwan burukan mu take ba sani ba sabo, wanda hakan ya isa ya shaida wa bawa, wannan kalma ta, "Tun ran gini tun ran zane", wato bawa ba ya tsallakewa Ƙaddararsa.Sarki ya yi wa Baiwa alƙawarin abinda ke cikinta sai ya mulki MASARAUTAR BAHJA har ma ya kai ga kanzaƙin raɗa wa abun cikin suna tun bai shaƙi iskar duniya ba, sai dai kuwa yayi shuka ne a idon makorwa, da saninsa ko ba da saninsa ba ma ce ba, domin masu haƙiƙanin gadon sarautar sun ce sa ji sa gani ta yadda za a binne tsohuwa da ranta.To jama'a, ga dai buruka da muradai, amma kuma ba wanda ya san me alƙalamin ƙaddara ta riga da ta zana tun fil'azal.  YARIMA BAHJAT, waye Yarima Bahjat?Masarautu uku ne, kuma mabanbanta, ɗaya bai yi kamanceceniya da ɗaya ba a ta ko wace fiska,...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters16
premium7
10

Shafi na sha biyu

Premium
Updated 11 days agoAvailable now
11

Shafi na goma

Premium
Updated 11 days agoAvailable now
12

Shafi na sha ɗaya

Premium
Updated 11 days agoAvailable now
13

Shafi na sha uku

Premium
Updated 11 days agoAvailable now
14

Shafi na sha huɗu

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
15

Shafi na sha biyar

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
16

Shafi na sha shida

Premium
Updated a day agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play