FreeArewaPen original
LIKITAN RUHI BOOK 2
- 1views
- 125chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writer
Sample · SHAFI NA ARBA’IN DA SHIDA
LIKITAN RUHI BOOK 2 Na ZAINAB BAWA Arewabook @Zeeeyybawa Marubuciyar BIBIYATA AKEYI SHAFI NA ARBA'IN DA SHIDA Sai wajen misalin ƙarfe tara Mami ta tashi daga bacci, domin ta raba dare tana yi wa Hammad addu'ar samun sauƙi, Bayan ta tashi, ta yi wanka ta shirya sannan ta fito falo, Masu aiki ne kawai suke ta zirga-zirga a lokacin, don haka ta fito zuwa waje. A zuciyarta ta ji kamar ta je ta duba jikin Hammad, amma sai ta tuna cewa yana tare da matarsa a wannan lokacin, Kuma tunda ba a ji shiru, hakan yana nufin yana lafiya, domin Ameerah a tare da shi, kuma idan akaji shiru toh lafiya ce domin ita ke ɓuya. Sai ta nufi sashen da aka sauƙi su Yaa Mu'azzam, domin ta duba jikin Fatima. A bakin ƙofar ta yi knocking, amma tana iya jiyo maganarsu a ciki, Yaa Madu ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar. Da ya ga Mami, sai ya saki murmushi yana faɗin. "Shigo Mami." Mami ta shiga ciki, Bayan ta zauna, Yaa Mu'azzam ya ce: "Ina kwana, Mami?" Mami ta amsa. "Lafiya ƙalau. Mu'azzam, ya mai jiki da Jannah?" "Da sauƙi. Tana ciki tana bacci." "Ma sha Allah. Allah ya ƙara mata lafiya." "Amin," suka amsa gaba ɗaya. Yaa Madu ma ya gaida Mami, ta amsa masa, Mami ta ɗan nisa kafin ta ce: "Babu wani abu da ya faru jiya da daddare ko?" Yaa Mu'azzam ya girgiza kai. "Babu abunda ya faru, Tunda Ameerah ta ce mu kunna karatu, ko razanar da take yi cikin dare bata yi ba, Sannan nima kusan kwana nayi ina sallah. Alhamdulillah, har zuwa yanzu dai komai lafiya." Mami ta jijjiga kai tace. "Toh mungodewa Allah, Yanzu next step ɗin sai mu jira Ameerah ta tashi kafin mu san abun yi ko?" Yaa Madu ne ya amsa da. "Ai Mami, inaga Ameerah kam ta tashi, Ko ince bata yi bacci ma gabaki ɗaya, domin bata bacci, Mu kirata kawai sai ta faɗa mana abun yi." Mami ta kalleshi da ɗan mamaki tace. "Bata bacci? Kuma me ya sa?" Yaa Mu'azzam ne ya bata amsa. "Mu kanmu Mami ba mu sani ba. Amma bata iya yin bacci, Gara kwanaki da Madu ya shiga damuwa sosai bayan ya fahimci hakan, sannan ya matsa akan lallai sai likita ya dubata, domin ba lafiya ba ne, ace mutum ya kasance baya iya bacci. Sai tace idan ta je asibiti tana iya yi, sanin bata ƙarya yasa muka yarda cewa tana yi a can ɗin" Mami ta kalli Yaa Madu tace. "Haka aka haifeta kenan, ko daga baya ta samu?" "Gaskiya daga baya ne, amma ba za mu iya faɗin dai-dai lokacin ba, Saboda da zarar dare ya yi take kulle ƙofofin ɗakinta, bata buɗewa sai safiya, Babu wanda ya san abunda yake faruwa, bayan ta koma gidan Mama Hajiya ne aka gano cewa kwata-kwata bata bacci, An tambayeta tun yaushe, amma bata faɗa wa kowa ba, Inaga dai tsawon lokacin da aka san bata bacci zai iya kaiwa shekara bakwai."Mami ta zaro ido a ɗan tsorace, a ranta tana ji Lallai akwai wani abu mai girma da yake damun Ameerah a fili kuma tace. "Ameerah bata iya bacci sai ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.